Sabon Kudiri: Ana Son Shugaban Kasa Ya Dawo Yin Shekara 6 babu Tazarce a Najeriya

Sabon Kudiri: Ana Son Shugaban Kasa Ya Dawo Yin Shekara 6 babu Tazarce a Najeriya

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce zai gabatar da kudirin wa’adin shekara shida ba tazarce
  • Sanata Bamidele ya ce tsarin zai bai wa shugaban kasa, gwamnoni damar mayar da hankali kan aiki maimakon neman tazarce
  • Rahotanni sun bayyana cewa kudirin da sanatan na Ekiti ke shirin gabatarwa zai bukaci gyaran kundin tsarin mulki kafin ya fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya na shirin gabatar da sabon kudirin doka da zai sauya tsarin kudin mulkin Najeriya.

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa zai gabatar da kudurin dokar da zai tanadi wa’adin shekara shida ba tazarce ga shugaban kasa da gwamnoni bayan zaben 2027.

Dan majalisar dattawa zai gabatar da kudirin kayyade mulkin shugaban kasa zuwa shekara 6 ba tazarce
Zauren majalisar dattawan Najeriya da ke babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Dalilin neman wa’adin shekara 6

Bamidele ya bayyana cewa kudirin zai kasance cikin farkon dokokin da yake son gabatarwa idan aka kafa Majalisar dattawa ta 11 bayan babban zabe mai zuwa, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta kashe Naira biliyan 10, Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa a yaki Ebola

Da yake magana da manema labarai a ofishinsa ranar Talata, Bamidele ya ce tsarin wa’adi biyu na yanzu yana sa shugabanni su shafe lokaci mai yawa suna shirye-shiryen sake zabe maimakon mayar da hankali kan mulki.

Ya ce:

“Daya daga cikin dokokin farko da nake son gabatarwa idan Allah ya kai mu majalisar dattawa ta 11 shi ne kudirin da zai bai wa duk wanda ya zama shugaban kasa ko gwamna damar yin wa’adi daya na shekara shida kacal.”

Sanatan ya ce tsarin zai rage siyasar neman tazarce da ke dauke hankalin shugabanni daga gudanar da ayyukan gwamnati.

“Shugabanni za su fi maida hankali kan aiki”

A cewar Bamidele, idan shugaba ya san cewa shekara shida kacal zai yi, zai yi kokarin amfani da damar yadda ya kamata tun daga ranar farko.

“Ba za ka bata kusan shekara daya da rabi kana tunanin yadda za a sake zabarka ba. Idan ka san wa’adi daya ne kawai, za ka yi bakin kokarinka tun daga rana ta farko,” in ji Bamidele.

Jaridar The Nation ta rahoto sanatan ya kara da cewa wannan zai taimaka wajen inganta shugabanci da aiwatar da manufofi cikin natsuwa.

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

Shugaban masu rinjayen ya amince cewa ba kowa ne zai yarda da kudirin ba, amma ya ce aikin ‘yan majalisa ne su gabatar da sauye-sauyen da suke ganin za su amfani kasa.

Sanata Opeyemi Bamidele ya ce zai gabatar da kudurin kayyade mulkin shugaban kasa zuwa shekaru 6 ba tazarce.
Sanata Opeyemi Bamidele, dan majalisar dattawan da ke shirin gabatar da kudurin kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa zuwa shekara 6. Hoto: @mob_sen_leader
Source: Twitter

Ana bukatar gyaran kundin tsarin mulki

Rahotanni sun nuna cewa idan aka gabatar da kudirin kuma majalisar tarayya ta amince da shi, sai an yi gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya kafin ya fara aiki.

Masana siyasa na ganin irin wannan kudiri na iya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da sauran ‘yan Najeriya.

An dade da bukatar takaita wa'adin mulki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, lauyoyi da ‘yan rajin dimokuradiyya na son a takaita wa’adin mulki zuwa guda na shekara shida don hana asarar kudade.

Wasu daga cikin masu fafutukar sun ce hakan zai rage amfani da dukiyar jama’a da shugabanni ke yi a yakin neman zaben tazarce bayan wa'adin farko.

Sai dai duk da haka, wasu na ganin karin wa’adi ga shugabanni na inganta tsarin aikin gwamnati da fahimtar matsalolin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com