Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 10, Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa a Yaki Ebola

Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 10, Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa a Yaki Ebola

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sakin N10bn domin shirin dakile yiwuwar barkewar cutar Ebola a Najeriya
  • Gwamnatin tarayya za ta kafa kwamitin shugaban kasa karkashin Femi Gbajabiamila domin jagorantar shirin yakar cutar
  • Najeriya ta kara tsaurara matakan tsaro da bincike a filayen jiragen sama bayan an samu bullar Ebola a Uganda da DR Congo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sakin Naira biliyan 10 a matsayin kudin gaggawa domin karfafa shirye-shiryen Najeriya kan yiwuwar barkewar cutar Ebola.

Naira biliyan 10 da Tinubu ya amince a kashe za su taimaka wajen inganta tsarin kariyar lafiya na kasa da kuma karfafa martanin gaggawa idan aka samu bullar cutar.

Tinubu ya amince a kashe N10bn domin yaki da barkewar cutar Ebola a Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu ya kafa kwamitin yaki da Ebola

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X ranar Talata.

Sanarwar ta ce shugaban kasar ya kuma amince da kafa kwamitin shugaban kasa kan shirin dakile cutar Ebola da sauran barazanar lafiyar jama’a.

An bayyana cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne zai jagoranci kwamitin tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya da wakilan jihohi.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin ya biyo bayan bullar sababbin cututtukan Ebola da aka samu a kasashen Uganda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

An tsaurara bincike a filayen jirage

Najeriya ta bayyana cewa ta fara kara tsaurara bincike a kan iyakoki da filayen jiragen sama domin hana shigowar cutar cikin kasar.

Sanarwar ta ce:

“Za a kara tsaurara binciken fasinjoji a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa, ciki har da duba zafin jiki da matakan kula da cunkoso.”

Hukumomin da za su jagoranci aiwatar da matakan sun hada da FAAN, Hukumar Shige da Fice ta Najeriya da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta NCAA.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya

Matakan kariya da gwamnati ta dauka

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a rika sa ido sosai kan fasinjojin da ke shigowa daga yankunan da ake ganin suna da hadarin barkewar Ebola.

Haka kuma an ce an tanadi cibiyoyin killace masu dauke da cuta a filayen jiragen sama na Lagos da Abuja.

Daga cikin sababbin matakan akwai wajabta cike bayanan lafiya ga matafiya da kuma tsaftace wuraren sauke kaya da jakunkuna akai-akai.

Rahotanni sun nuna cewa NCDC ce za ta kula da shirin dakile yiwuwar barkewar Ebola a Najeriya.
Ma'aikatan lafiya na duba wasu marasa lafiya da aka killace yayin COVID-19 a Najeriya. Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

NCDC za ta jagoranci aikin

Rahotanni sun nuna cewa babban bangaren kudaden zai tafi ne ga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Gwamnatin ta ce kwamitin shugaban kasa zai hada kai da hukumomin tsaro, sufurin jiragen sama da diflomasiyya domin tsara yadda jirage daga yankunan da aka samu Ebola za su rika sauka.

An kuma bayyana cewa za a ware tashoshi na musamman domin karbar matafiya daga yankunan da ake da hadarin barkewar cutar.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Ana tsoron barkewar Ebola a Najeriya

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar NCDC ta sanya Legas, Kano, Rivers da wasu jihohi cikin shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola.

Hakan na zuwa ne bayan da aka ayyana yiwuwar shigowar nau’in cutar Bundibugyo Ebola zuwa tarayyar Najeriya bayan ta bulla a Afrika.

NCDC ta yi gargadi da cewa dole Najeriya ta gaggauta karfafa tsarin sa ido, wuraren killace masu dauke da cutar da matakan kariya daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com