Hukumar Lafiya ta duniya watau WHO, ta saki matsayin kasar Najeriya da makwabta kan sabuwar bullar cutar Ebola
A sakamakon barkewar cutar Ebola a Congo, kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta lisssafo kasar Najeriya da wasu kasashen Afirka a matsayin masu tsaka tsakin damar kwasar kwayar cutar.
NCDC, ta bayyana hakan a wata maganar ta a ranar asabar, inda hukumar ke Jan kunnen 'yan Najeriya dasu kiyaye kuma su bi hanyoyin gujewa barkewar cutar a kasar.
Kamar yanda rahoton WHO yace, mutane 16 ne suka rasa rayukansu a kasar Congo sakamakon barkewar cutar.
Malaman kiwon lafiya guda uku ne suka rasa rayukansu. Wannan shine Karo na tara da samun cutar a jamhuriyar Congo din.
DUBA WANNAN: Ya dauki karuwa zasu hutu kasar waje, matarsa ta kama su a filin jirgi
Barkewar cutar mafi muni da ta zo karshe ne a Afirka ta yamma shekaru biyu da suka wuce. Inda cutar tayi ajalin mutane 11,300 da kuma mutane, 28,600 da ta sama. Kwayar cutar ta shiga kasar Guinea, Sierra Leone da kuma Liberia.
A watan Disamba, 2013,bayan da yaro Dan shekaru 2 a duniya ya mutu sakamakon cutar Ebola din a wani kauye a Guinea, cutar ta yadu zuwa kasashen Afirka ta yamma, ta iso Najeriya, Spain da Amurka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng