Ana Tsoron Bullar Cutar Ebola Mai Hadari a Kano, Borno da Wasu Jihohin Najeriya

Ana Tsoron Bullar Cutar Ebola Mai Hadari a Kano, Borno da Wasu Jihohin Najeriya

  • Hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanya Legas, Kano, Rivers da wasu jihohi cikin shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola
  • Hakan na zuwa ne bayan da aka ayyana yiwuwar shigowar nau’in cutar Bundibugyo Ebola zuwa tarayyar Najeriya bayan ta bulla a Afrika
  • NCDC ta yi gargadi da cewa dole Najeriya ta gaggauta karfafa tsarin sa ido, wuraren killace masu dauke da cutar da matakan kariya daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar NCDC ta sanya Kano, Legas, Abuja da wasu jihohi cikin shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola bayan barkewar mummunar nau’in cutar a wasu sassan Gabashi da Tsakiyar Afirka.

A cikin sanarwar lafiya ta kasa da ta aika wa kwamishinonin lafiya a fadin kasar, hukumar ta gargadi cewa Najeriya na cikin hadarin shigowar cutar saboda karuwar yaduwar ta a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

An samu barkewar cuta a Borno, fiye da mutane 25 sun mutu a cikin watan nan

Likitoci a bakin aiki a kasar Congo
Likitocin kasar Congo da ke aikin yaki da cutar Ebola. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa hukumar NCDC ta ce zirga-zirga tsakanin kasa da kasa, iyakoki marasa dokoki masu tsauri da kuma tafiye-tafiyen jama’a na cikin abubuwan da za su iya haddasa yaduwar cutar.

Ebola: Jihohin da aka yi wa gargadi

Sanarwar mai dauke da kwanan wata 27 ga Mayu, 2026, ta zo ne yayin da ake kara nuna damuwa kan yaduwar nau’in Bundibugyo na Ebola da ba kasafai ake samu ba wanda har yanzu babu ingantaccen allurar rigakafi ko maganinsa.

Jihohin da NCDC ta ayyana a matsayin masu hadari sun hada da Legas, Rivers, Kano, Enugu, Borno, Akwa Ibom, Cross River, Taraba da Adamawa da kuma birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce cutar za ta iya bulla a jihohin ne saboda filayen jiragen sama na kasa da kasa da suke da shi, tashoshin ruwa, iyaka da kasashe da yawan zirga-zirgar jama’a.

Har yanzu babu Ebola a Najeriya

Vanguard ta wallafa cewa hukumar NCDC ta bayyana cewa har yanzu ba a samu wani tabbataccen mutum ko da daya ne mai dauke da cutar ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar salla: Tinubu ya saukaka wa yan kasa, ya rage kudin sufurin jiragen kasa

Sai dai ta ce wani binciken tantance hadari da aka gudanar bayan ayyana barkewar cutar a matsayin matsalar lafiya ta duniya ya nuna cewa yiwuwar shigowar cutar Najeriya har yanzu na da yawa.

A cewar NCDC, an riga an samu mutane 1,077 da ake zargi sun kamu da cutar tare da mutuwar mutum 247 a Uganda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, inda kaso 24.6 cikin 100 ke mutuwa.

Ta kara da cewa cutar ta haddasa damuwa a duniya, inda aka ce an gano wasu wadanda ake zargi da cutar a Indiya, yayin da Canada ta sanar da takaita wasu bukatun tafiye-tafiye daga mazauna Uganda, DRC da Sudan ta Kudu na wani lokaci.

Ministan lafiya na Najeriya, Ali Pate
Ministan lafiya, Ali Pate a ofishinsa a Najeriya. Hoto: @Fmohnigeria
Source: Twitter

Kwalara ta yi kisa a Borno

A wani labarin, mun kawo muku cewa an sanar da cewa sama da mutum 2,000 ne suka kamu da cutar kwalara a jihar Borno a watan Mayun 2026.

Bayanin da gwamnati ta fitar ya nuna cewa sama da mutum 20 sun rigamu gidan gaskiya a fadin jihar yayin da wasu ke kwance a asibiti.

Jami'an lafiya sun bukaci mutane da su rika bin matakan da aka gindaya domin tsira da lafiyar su, musamma a lokacin bikin sallar layya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng