"Ku Yi Murabus cikin Mutunci," Majalisar Wakilai Ta ba Hafsoshin Tsaron Najeriya Zabi 2
- Majalisar Wakilai ta tarayya ta bukaci hafsoshin tsaro su sauka daga mukamansu cikin mutunci idan ba za su iya matsalar tsaro ba
- 'Yan majalisar sun nemi shugaban kasa Bola Tinubu ya fito da sabon tsari mai karfi na yaki da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane
- Majalisar ta nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa makarantu da wuraren ibada da kuma sace dalibai a sassan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta Tarayya ta gargadi hafsoshin tsaro da su yi murabus cikin mutunci idan har sun san ba za su iya shawo kan tabarbarewar tsaro a kasar nan ba.
Majalisar ta kuma bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fito da tsari mai karfi da zai kawar da 'yan bindiga, 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane daga maboyarsu a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Dalilin Majalisa na daukar mataki
Vanguard ta ce wannan matsaya ta biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da 'dan majalisa mai wakiltar Arochukwu/Ohafia ta jihar Abia, Hon. Ibe Osonwa, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.
Kudirin ya mayar da hankali ne kan karuwar hare-haren 'yan bindiga, sace-sacen dalibai da kuma matsalar tsaro da ta dabaibaye makarantu da wuraren ibada a fadin kasar nan.
Osonwa ya jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wa gwamnati alhakin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya yi nuni da sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulkin 1999 wanda ya tanadi cewa tsaro da jin dadin jama'a su ne babban nauyin da ke kan gwamnati.
Majalisa ta koka kan satar dalibai
'Dan majalisar ya bayyana cewa yawaitar sace dalibai daga makarantu ta kara jefa bangaren ilimi cikin matsala, tare da kara adadin yara marasa zuwa makaranta.
A cewarsa, dubban yara sun daina zuwa makaranta saboda tsoron hare-hare, yayin da iyalai da dama ke ci gaba da fama da radadin sace 'ya'yansu, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya
Ya kuma nuna damuwa cewa makarantu da wuraren ibada, wadanda a baya ake dauka a matsayin wurare masu aminci da kwanciyar hankali, yanzu sun zama wuraren da mahara ke kai wa hari cikin sauki.
Abin da Majalisa ta bukata daga Tinubu
Bayan muhawara, Majalisar Wakilai ta yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kai farmaki kan makarantu da coci-coci a Najeriya.
Majalisar ta bukaci shugaban kasa Tinubu ya gaggauta aiwatar da wani tsari mai tsauri domin rushe sansanonin 'yan bindiga, kare makarantu da wuraren ibada da ceto duk mutanen da ke hannun masu garkuwa ba tare da sharadi ba.

Source: Facebook
Haka kuma, kwamitocin majalisar kan tsaro, leken asiri da rundunar soji sun samu umarnin sa ido kan aiwatar da wadannan matakai tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu domin daukar karin matakai.
Majalisa za ta binciki hare-haren Borno
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta waiwayi hare-haren da ƴan ƙungiyar ta'addanci na Boko Haram suka kai sansanonin sojoji a Borno.
Majalisar Dattawa ta ba wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, tare da sauran shugabannin rundunonin tsaro umarni da su gudanar da cikakken bincike hare haren.
Majalisa ta bukaci a yi nazari mai zurfi kan yadda hare-haren suka faru, daga ciki har da tantance wadatar kayan aiki da kuma bin ka’idojin aiki na rundunar soji.
Asali: Legit.ng
