Kamar Tubabbun 'Yan Boko Haram: Gumi Ya Nema wa 'Yan BIndiga Afuwa

Kamar Tubabbun 'Yan Boko Haram: Gumi Ya Nema wa 'Yan BIndiga Afuwa

  • Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi wa ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka yi wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram
  • Malamin ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai bai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta shafe akalla shekaru 17 ana addabar jama'a da kashe rayuka
  • Sheikh Ahmad Gumi ya musanta zarge-zargen cewa yana goyon bayan ta’addanci ko ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba hanyoyin da take bi wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Fitaccen malamin ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta yi wa ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka yi wa tubabbun mayaƙan Boko Haram.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Sheikh Gumi ya nema wa tubabbun yan bindiga afuwa
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa da Sheikh Ahmad Gumi Hoto: HQ Nigerian Army/Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a gidansa da ke Kaduna ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2026.

Gumi ya nema wa yan bindiga afuwa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Malamin ya ce gwamnatin Najeriya ta dade tana amfani da ƙarfin soji wajen yaƙi da ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya, amma har yanzu matsalar ba ta kau ba.

A cewarsa, idan hanyar amfani da makamai da hare-haren soji ba ta yi aiki ba tsawon shekaru 17, akwai bukatar gwamnati ta sauya salo tare da rungumar hanyoyin sulhu da gyaran rayuwa.

Ya ce:

“Idan hanyar amfani da ƙarfi ba ta yi aiki ba tsawon shekaru 17, me ya sa ba za a canja hanya ba? Mu sauya tsarin.”

Gumi ya kuma ce akwai bukatar a fito da ‘yan bindiga daga dazuzzuka tare da samar wa yaransu ilimi da walwala domin hana ci gaba da shiga harkokin ta’addanci.

Kara karanta wannan

'Babu afuwa': Babban limami ya fadi abin da Kur'ani ya ce kan yan ta'adda

A cewarsa, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun nuna shirinsu na ajiye makamansu idan gwamnati ta ba su tabbacin cewa ba za a kama su ko a muzanta su ba bayan sun mika wuya.

Gumi ya musanta goyon bayan ta’addanci

Malamin ya ce gwamnati ba ta mayar da hankali sosai kan shirye-shiryen gyaran hali da sake haɗa tubabbun mayaƙa cikin al’umma ba duk da yawan waɗanda suka mika wuya a shekarun baya.

Ya ce wasu daga cikin ‘yan bindiga sun bayyana masa cewa tsoron kama su ko gallaza masu ne ke hana su ajiye makamai.

Sheikh Gumi ya ce yan bindiga suna tsoro
Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen makamin addinin Musulunci a Najeriya Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Saboda haka, ya nemi gwamnati ta samar da tsarin afuwa domin ƙarfafa musu gwiwar daina ayyukan ta’addanci.

Sai dai Gumi ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa na goyon bayan ta’addanci ko kare ‘yan bindiga. Ya ce duk wani bidiyo, rubutu ko saƙon da ake dangantawa da shi wanda ke nuna yana goyon bayan ta’addanci ba daga gare shi ya fito ba ne.

Barazanar Gumi kan alakanta shi da yan bindiga

A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya musanta cewa yana goyon bayan ’yan bindiga da ke ta'addanci tare da kashe bayin Allah a kasar.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi barazana ga masu alakanta shi da goyon bayan 'yan bindiga

Fitaccen malamin ya bayyana cewa kawai wasu kungiyoyi da mutane da ke juyar da kalamansa da gangan saboda wata bukatar kashin kansu, amma babu lokacin da ya goyi bayan a'yan bindiga.

Sheikh Ahmad Gumi ya kara da cewa daga yanzu ba zai bar lamarin haka ba, zai dauki mataki na shari'a domin a bi masa hakkinsa a kan wadannan zarge-zarge da kokarin bata masa suna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng