Ambaliya: Abin da Sanatocin Arewa ke Bukata daga Tinubu da Gwamnatin Neja

Ambaliya: Abin da Sanatocin Arewa ke Bukata daga Tinubu da Gwamnatin Neja

  • Yan Majalisar Dattawan Arewa sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja su waiwayi batun ambaliyar ruwa a Shiroro da ake samu duk shekara
  • Sun nemi a samar da cikakken tsarin kula da ambaliyar Shiroro, tare da tsarin hasashen ambaliya da gargadin gaggawa kafin kwararowar ruwan
  • Sanatocin sun ce bala’in Mokwa na 2025 da binciken da ya nuna cewa kashi 32 cikin 100 na Shiroro na fuskantar barazanar ambaliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Majalisar Dattawan Arewa ta yi kira da a samar da mafita ta dindindin kan yawan ambaliyar ruwa da ke addabar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Sanatocin sun bukaci Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Neja su dauki matakan dogon lokaci domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ke haddasawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Yadda gwamnatin Sokoto ta shirya sayo baburan Naira biliyan 2

Sanatoci sun nemi a kawokashen ambaliya a Neja
Sanata AbdulAziz Yar'adua @AbdulazizYaradua
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa Shugaban Majalisar Dattawan Arewa, Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 12 ga watan Agusta, 2026.

Kiran Sanatoci ga gwamnati

Jaridar The Guardian ta kawo labarin cewa Sanatocin sun bukaci a samar da tare da aiwatar da cikakken tsarin kula da ambaliyar Shiroro, wanda zai kasance jagora wajen tunkarar matsalar ambaliyar da ke faruwa akai-akai.

Sun ce tsarin ya kamata ya kunshi dabarar kimiyya da za a yi amfani da ita wajen sarrafa yawan ruwan da ake saki daga madatsun ruwa na Shiroro, Kainji da Jebba.

Haka kuma, sun bukaci a samar da tsarin dindindin na hasashen ambaliyar ruwa da gargadin gaggawa, tare da horar da ’yan sa-kai na cikin al’umma da za su taimaka wajen sanar da mutanen da ke zaune a yankunan da ke kasa da madatsun ruwan.

Kara karanta wannan

1448: Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa ana shirin shiga watan Maulidin Annabi SAW

Sanatoci sun shiga maganar yan gudun hijira

Sanatocin sun kuma nemi a samar da cikakken shirin sake tsugunar da mutanen da ambaliyar ke shafa, wanda zai hada da gina sabbin matsugunai, biyan diyya da kuma tallafawa wadanda abin ya shafa wajen samun abin dogaro da kai.

Ana son gwamnatin Neja da ta Bola Tinubu su waiwayi Shirori
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago Hoto: Umaru Bago
Source: Facebook

Majalisar ta kuma bukaci a gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan yadda ake tafiyar da madatsun ruwa, karfin tafkunansu da kuma yadda hanyoyin fitar da ruwa ke aiki, musamman bisa la’akari da sauyin yanayin da ake samu a yanzu.

Sanatocin sun ce hakan zai taimaka wajen gano yadda za a rika sarrafa sakin ruwa a nan gaba domin rage hadarin ambaliyar ruwa a al’ummomin da ke kasa da madatsun.

Sun yaba wa Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) kan daukin da ta kai da kuma raba kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa.

Ana fargabar ambaliya

A baya, mun kawo labarin cewa ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar da gargadi cewa jihohi tara da yankuna 14 a Arewa na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin 25 zuwa 29 ga Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027

Gargadin ya fito daga Cibiyar Gargaɗi kan Ambaliya, inda aka bukaci mazauna kauyuka a gabar Kogin Neja daga Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta barin yankunan kafin lokacin ambaliyar ya zo.

Jihohin da abin zai shafa sun hada da Adamawa, Borno, Gombe, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, inda aka bayyana kauyuka da dama cikin hatsarin ambaliya wanda ya dade yana salwantar da rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng