‘Yadda Aka Yi wa Jonathan’: Malami Ya Hango Makarkashiya ga Tinubu a 2027

‘Yadda Aka Yi wa Jonathan’: Malami Ya Hango Makarkashiya ga Tinubu a 2027

  • Limamin Katolika, Fasto Ejike Mbaka, ya yi magana game da sace ɗaliban Oyo inda ya ce akwai wata manufa ta siyasa
  • Mbaka ya kwatanta lamarin da sace 'yan matan Chibok na 2014, yana mai cewa an sake amfani da irin wannan dabara
  • Ya gargadi 'yan Najeriya kada su ruɗu, yana mai cewa masu daukar nauyin irin waɗannan ayyuka suna neman haifar da firgici

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu - Faston Katolika, Ejike Mbaka, ya yi watsi da sace ɗalibai 46 da malamai a Oyo, yana mai cewa wata manufa ce ta siyasa.

Mbaka, wanda shi ne wanda ya kafa cocin Adoration Ministries a Enugu, ya ce an shirya hakan ne domin hada 'yan Najeriya da gwamnati.

An hango shirin makarkashiya kan Tinubu kamar yadda aka yi wa Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Bola Tinubu. Hoto: Goodluck Jonathan, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne na faston a wani bidiyo da ya yadu wanda YabaLeftOnline ya yada a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

Sace dalibai: Fasto ya ba gwamna shawara

Malamin ya bayyana damuwa game da karuwar rashin tsaro inda ya ce bai kamata a tsoma satar yara dalibai cikin lamarin ba, cewar Daily Post.

Ya ce Gwamna Seyi Makinde ya tashi tsaye, tare da kira ga 'yan Najeriya su mayar da hankali kan abin da ke faruwa.

Malamin ya kwatanta sace yaran Oyo da sace 'yan matan Chibok a 2014, yana mai cewa dabara iri ɗaya ce.

Ya ce an yi amfani da irin wannan salon ne a kan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kafin zaɓen 2015.

Mbaka ya ce:

"Idan suna son hambarar da Tinubu, ba ta hanyar sace yaranmu ba ne domin fusata 'yan Najeriya.
"Sun sake yin hakan, kada 'yan Najeriya su bari a yaudare su. Wannan wata muguwar manufa ce ta siyasa."
Tinubu ya damu bayan sace dalibai a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yayin ziyara a birnin Yenagoa da ke Bayelsa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Abin da fasto ke hasashe kan rashin tsaro

Mbaka ya ce ana ƙoƙarin jefa tsoro cikin ƙasa domin jama'a su nemi shugaban ƙasa ya sauka daga mulki, cewar Peoples Gazette.

Kara karanta wannan

Babu zancen shari'ar Musulunci: Ƴan bindiga da suka sace dalibai a Oyo sun fadi bukatunsu

Kafin zaɓen 2015, Mbaka ya jagoranci yaƙin neman sauyi tare da sukar Jonathan da yi masa laƙabin "bad luck."

A lokacin, ya yi kira ga 'yan Najeriya su rungumi sauyi, yana cewa ƙasar na buƙatar sabon shugabanci domin kawo karshen tsaro a wancan lokaci.

Ya bayyana cewa rashin tsaro, matsalar tattalin arziki da sauran ƙalubale ne suka sa ya yi wannan kiran sauyi saboda halin da yan kasa ke ciki a mulkin Jonathan.

Tinubu ya yunkuro kan matsalar tsaro

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ba za ta mika wuya ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka da ke ƙoƙarin tsoratar da ƙasar ba.

Ya sake jaddada alƙawarin gwamnatinsa na murƙushe masu tayar da hankali da kuma tabbatar da kuɓutar da dukkan ’yan Najeriya da ake tsare da su.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓukan shekara mai zuwa, ya kamata ’yan Najeriya su guji tashin hankali kan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.