Dakarun Sojoji Sun Hallaka Jagororin 'Yan Bindiga a Zamfara, an Kashe 'Yan Ta'adda
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarori kan 'yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina bayan sun gwabza fada
- Sojojin sun samu nasarar hallaka wasu jagororin 'yan bindiga bayan sun yi artabu da su a karamar hukumar Anka ta Zamfara
- Sojojin ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kwato makamai da babura daga hannun 'yan bindigan da suka tura zuwa barzahu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dakarun 'Sector 2' na rundunar sojojin kasa ta Najeriya sun kashe wasu manyan jagororin ’yan bindiga, Anaruwa da Gomina.
Sojojin sun hallaka jagororin ne tare da wasu mutane bakwai a jerin ayyukan tsaro da aka gudanar a cikin kwanaki uku da suka gabata a jihohin Zamfara da Katsina.

Source: Twitter
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa mukaddashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na 'Sector 8' ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.
Sojoji sun kashe jagororin 'yan bindiga
Ya bayyana cewa a jihar Zamfara, dakarun sojoji da ke sansaninsu na Bagega sun gudanar da wani babban aiki a ƙaramar hukumar Anka, wanda ya kai ga kashe ’yan ta’adda bakwai, ciki har da wasu manyan jagorori biyu da aka gano a matsayin Anaruwa da Gomina.
Anaruwa ƙani ne ga Kachalla Idi Aiki, wani sanannen kwamandan ’yan ta’adda ne da ya addabi jama'a.
Laftanar Kanar Olaniyi ya ci gaba da bayyana cewa, a yayin aikin farko, dakarun sun yi artabu da ’yan ta’adda a kan hanyar Bagega zuwa Anka.
“Artabun farko ya tilasta wa ’yan ta’adda hudu ɗauke da makamai a kan babura biyu ja da baya, inda suka bar baburansu. Sai dai ’yan ta’addan sun sake haɗuwa tare da kai harin ramuwar gayya a sansanin Bagega."
- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba
Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A cewarsa, bayan samun tallafin dakarun yaƙi daban-daban tare da taimakon hare-haren sama na, dakarun sun dakile harin yayin da suka fafata da wasu ’yan ta’adda takwas a kan babura hudu, wanda hakan ya kai ga kashe ’yan ta’adda uku.
“Yayin aikin, dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu mai ɗauke da harsasai da kuma babura bakwai."
- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba
Bisa bayanin sanarwar, yayin wani aikin daban a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2026, dakarun sun ci karo da wasu ’yan ta’adda biyu a kan babura a yankin, inda aka kashe su nan take, jaridar TheNation ta kawo rahoton.

Source: Twitter
Sojoji sun samu nasara a Katsina
Olaniyi, yayin da yake bayyana nasarorin rundunar a jihar Katsina, ya ce dakarun sansanin Fudma, yayin aikin sintirin yaƙi, sun ci karo da ’yan ta’adda a kan hanyar Turare zuwa Yantumaki a ƙaramar hukumar Dutsinma.
“Dakarun sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda tara, ciki har da jagorori biyu sannan sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda hudu da babura tara a jihohin Katsina da Zamfara."
- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba
Sojoji sun kashe kwamandojin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka wasu kwamandojin 'yan ta'adda a Katsina.
Dakarun sojojin sun kashe mutane hudu da ake zargi ’yan ta’adda ne yayin aikin sintiri a kan hanyar Turare zuwa Yantumaki.
Jami’an tsaro sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya mai ɗauke da harsasai biyar masu kaurin 7.62mm, babura biyu, wayoyin hannu da dama, da tsabar kuɗi har N153,400.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

