Yan Bindiga Sun Kashe Kansila da Babban Darakta a Zamfara Kwanaki 10 da Sace Su
- 'Yan ta'adda sun kashe Kansila a Zamfara da wani Daraktan Tsare-tsare na wata karamar hukuma a jihar
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun yi ajalin kansilan da abokin tafiyarsa ne bayan rena kudin fansa da aka ba su
- Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Yahaya Yari, ya ce an tattauna kan kudin fansa, amma 'yan ta'addar suka ki karba tare da kashe mutanen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Takata Mafara, Zamfara - 'Yan ta'adda sun kashe wani kansila da wani darakta na karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara.
Hakan ya biyo bayan kin karbar kudin fansa da aka ba su domin sakin su bayan kwanaki 10 da sace su.

Source: Original
Shugaban karamar hukumar, Yahaya Yari, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2026, cewar Premium Times.
Manyan mutanen da ƴan bindiga suka hallaka
Yahaya Yari ya ce wadanda aka kashe sun hada da Muslim Habibu, kansilan mazabar Jangebe, da Jamilu Sani, daraktan tsare-tsare na karamar hukumar Talata Mafara.
An yi garkuwa da su yayin da suke kan hanyarsu daga Jangebe zuwa hedikwatar karamar hukumar domin shirya harkokin aikin Hajji ga maniyyatan yankin Jangebe da ke shirin tafiya.
Marigayin da wani jami'in tara kudaden shiga na karamar hukumar suna tafiya ne daga Jangebe zuwa Mafara a ranar 18 ga watan Mayun 2026 lokacin da 'yan ta'addar suka kai musu hari.
Harin ya faru ne a kan hanyar Anka zuwa Mayanchi, inda jami'in tara kudaden shiga ya tsira duk da samun raunukan harsashi, amma sauran mutanen biyu suka fada hannun masu garkuwa, cewar rahoton Bakatsine.
Yahaya Yari ya bayyana hakan yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai wa iyalan mamatan a Talata Mafara, ya ce an fara tattaunawa kan kudin fansa tun bayan sace mutanen.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri

Source: Facebook
Yadda aka yi jana'izar wadanda suka mutu
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa a tattaunawa ta karshe da suka yi, masu garkuwar sun tabbatar musu cewa sun kashe mutanen biyu da aka sace.
Saboda ba a samu damar kwaso gawarwakinsu ba, an gudanar da sallar jana'izarsu daga can domin yi musu addu'a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Majiyoyi daga Talata Mafara sun ce 'yan ta'addan sun fusata ne saboda matakin da mutanen Jangebe da karamar hukumar suka dauka na bai wa Yan Sakai makamai.
Haka kuma an gayyato jami'an kungiyar CJTF daga Arewa maso Gabas domin taimakawa wajen yakar 'yan ta'addar da suka dade suna addabar yankin.
Wata majiya ta gwamnati ta ce a baya mutanen Jangebe sun yi nasarar kashe da dama daga cikin 'yan ta'addan bayan sun karfafa kungiyoyin tsaro na sa-kai.
Majiyar ta kara da cewa wannan ne ya sa 'yan ta'addan suka yanke shawarar cewa duk wanda suka sace daga Jangebe za su kashe shi maimakon karbar kudin fansa.
Sojoji sun kashen dan Ado Aliero
Mun ba ku labarin cewa sojojin Operation FANSAN YANMA sun hallaka fitattun shugabannin 'yan bindiga da dama ciki har da ɗan babban jagoran 'yan ta'adda Ado Aliero.
An yi amfani da jiragen yaƙi da dakarun ƙasa wajen murƙushe ƴan fashin dajin kusan 300 da suka yi ƙoƙarin tunkarar sojojin a cikin daji.
Masana tsaro sun yi gargaɗin cewa Ado Aliero na iya ƙoƙarin ɗaukar fansar mutuwar ɗan nasa, wanda hakan ya sa aka ƙarfafa tsaro a Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

