Alhazai Mata 2 daga Arewacin Najeriya Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Makkah

Alhazai Mata 2 daga Arewacin Najeriya Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Makkah

  • Rahotanni daga Saudiyya sun tabbatar da rasuwar wasu mata alhazai guda biyu daga Arewacin Najeriya
  • Majiyoyi suka ce mamatan sun rasu a Makkah bayan kammala aikin Hajjin 2026 cikin nasara ba tare da tasgaro ba
  • Wasu mata biyu da suka tsira daga hatsarin suna karɓar magani a asibitin Saudiyya, ɗaya na karayar ƙashi, ɗaya kuma na gocewar hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makkah, Saudi Arabia - Hukumomi daga kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa an samu rashin wasu daga cikin mahajjata mata daga Najeriya.

An ce mahajjata mata biyu daga Sokoto sun rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya bayan sun kammala aikin Hajjin shekarar 2026 cikin nasara.

Mahajjata daga Sokoto sun rasu a Makkah
Taswirar jihar Sokoto da aka yi rashin wasu mahajjata a Saudiyya. Hoto: Legit.
Source: Original

Mataimakin Amirul Hajj kuma Babban Alƙalin Sokoto, Alhaji Sodangi Acida, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Faruku Umar ya fitar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

An bayyana sunayen mamatan da Ladi Umar daga ƙaramar hukumar Bodinga da Hadiza Umar daga ƙaramar hukumar Yabo.

Acida ya ce wasu mahajjata mata biyu da suka shiga hatsarin suna ci gaba da karɓar magani a wani asibitin Saudiyya.

Ya ce ɗaya daga cikinsu tana jinya sakamakon karayar ƙashi, yayin da ɗayar kuma ke samun kulawa saboda gocewar hannu.

Ya miƙa ta'aziyyar gwamnatin Sokoto ga iyalan mamatan tare da addu'ar Allah Ya gafarta musu kura-kuransu.

Ya roƙi Allah Ya ba su Aljannatul Firdaus, tare da ba iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Mataimakin Amirul Hajj ya ce rukuni na farko na mahajjatan Sokoto zai tashi daga Saudiyya zuwa Najeriya ranar 14 ga Yuni.

Ya bayyana cewa za a gudanar da jigilar dawowar mahajjata ne bisa tsarin wanda ya fara zuwa shi zai fara tafiya.

Ya kuma buƙaci mahajjata su bi ƙa'idojin kayan da aka amince da su tare da kauce wa wuce ƙayyadadden nauyi.

Ya jaddada cewa kayan kowane mahajjaci bai kamata su haura kilo 32 da aka tanada ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yunkuro da karfi kan tsaro, zai murkushe 'yan ta'addan Najeriya

Sakataren dindindin na hukumar, Alhaji Ibrahim Umar JJ, ya yabawa Gwamna Ahmad Aliyu kan kulawarsa ga jin daɗin mahajjatan Sokoto.

Ya kuma yabawa mambobin tawagar jihar, shugabannin hukumar, ma'aikata da mahajjata saboda haɗin kai da goyon baya.

A cewarsa, irin wannan haɗin kai ne ya taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara ba tare da manyan matsaloli ba.

Karin bayani na tafe....

Wani Alhaji dan Bauchi ya rasu a Saudiyya

A baya, an ji cewa wani Alhaji dan Najeriya da aka ce dan asalin jihar Bauchi ne da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 ya rasu a Muzdalifah jim kadan bayan isowarsa daga Arafa.

Shaidu sun ce jami’an ‘yan sandan Saudiyya tare da ma’aikatan lafiya na gaggawa ne suka fitar da mamacin a kan keken daukar marasa lafiya jim kadan bayan faruwar lamarin.

Lamarin ya faru ne a lokaci mai wahala na aikin Hajji wanda ke tattare da yawan zirga-zirgar mahajjata tsakanin wurare masu tsarki karkashin tsananin yanayin zafi da dumbin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.