Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban UNILORIN Ya Rasu bayan Ya Dawo daga Sallar Isha'i

Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban UNILORIN Ya Rasu bayan Ya Dawo daga Sallar Isha'i

  • An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban jami'ar Ilorin (UNILORIN), Farfesa AbdulGaniyu Ambali da safiyar yau Asabar
  • Iyalansa sun bayyana cewa ya halarci sallar Isha'i a cikin jam'i a daren jiya Juma'a, amma rai ya yi halinsa da misalin karfe 3:00 na dare
  • Shugaban jami'ar Ilorin, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole ya mika sakon ta'aziyya, yana mai bayyana cewa Najeriya ta yi babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ilorin, Kwara, Nigeria - Tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Ilorin (VC), Farfesa AbdulGaniyu Ambali, ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen masanin ilimin dabbobi kuma gogaggen malamin jami’a ya rasu ne da sanyin safiyar Asabar a gidansa da ke Oloje Estate a Ilorin, jihar Kwara.

AbdulGaniyu Ambali.
Tsohon shugaban jami'ar UNILORIN da ke jihar Kwara, Farfesa AbdulGaniyu Ambali Hoto: Solihu O Yusuf
Source: Facebook

Rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa marigayin zai cika shekara 69 a watan Nuwamba mai zuwa, yana mai cewa ya rasu da misalin karfe 3:00 na safiyar yau Asabar.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya fadi dabarar kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban jami'ar UNILORIN ya rasu

Majiyoyi daga iyalinsa sun bayyana cewa Ambali ya rasu da misalin karfe 3:00, ‘yan sa’o’i bayan ya halarci sallar Isha’i a wani masallaci da ke kusa da gidansa a daren Juma’a.

Bayanai sun kuma nuna cewa babu wata rashin lafiya da aka san yana fama da ita mai tsanani kafin rasuwar tasa.

An shirya gudanar da sallar jana’izarsa (Janazah) da karfe 4:00 na yammacin yau Asabar a gidansa da ke Air Force Road, Oloje Estate, Ilorin.

Kakakin UNILORIN ya tabbatar da rasuwarsa

Mai magana da yawun UNILORIN, Kunle Akogun, ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa, inda ya ce Shugaban Jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN), ya sanar da rasuwar tsohon VC din.

Sanarwar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jami’ar Ilorin, Jihar Kwara da kuma kasa baki daya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaban jami’ar ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma al’ummar Ilorin, tare da kira ga mutane, musamman ma’aikatan UNILORIN, da su halarci sallar jana’izar da za a yi a gidansa da karfe 4 na yamma.

Kara karanta wannan

Tafiyar Atiku ta shiga matsala a Gombe, 'yan ADC sun koma APC da PDP

Unilorin.
Babbar kofar shiga jami'ar UNILORIN da ke jihar Kwara Hoto: UNILORIN
Source: Facebook

Takaitaccen tarihin marigayin

Farfesa Ambali ya rike mukamin shugaban jami’ar Ilorin na tara tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017.

Ya bar bayan babban tarihin aiki da ya shafe fiye da shekaru 30 a fannin koyarwa, bincike da kuma gudanar da harkokin jami’a.

Har zuwa lokacin rasuwarsa, shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Malete, matsayin da yake rike da shi bayan kammala wa’adinsa a Jami’ar Ilorin.

Malam Abbakar Pharmacy ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa matashin malamin addinin musulunci a jihar Gombe, Malam Abbakar Sadiq Pharmacy ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rasu ne a wani asibiti da aka kwantar da shi jihar Kano bayan ya yi fama da jinya.

Tsohon ministan sadarwa kuma 'dan takarar gwamnan Gombe a inuwar PDP, Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da rasuwar Malam Abbakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262