An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Mawaki a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Mawaki a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An shiga jimama bayan rasuwar fitaccen mawaki a Najeriya, Cif Daniel Iriferi a jihar Delta a yau Litinin
  • Marigayin wanda aka fi sani da Sally Young ya mutu ne a yau Litinin 12 ga watan Faburairu bayan fama da jinya
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Fitaccen mawakin Urhobo a Najeriya, Cif Daniel Iriferi ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 91.

Marigayin wanda aka fi sani da Sally Young ya mutu ne a yau Litinin 12 ga watan Faburairu bayan fama da jinya.

Fitaccen mawaki ya rasu ya na da shekaru 91
Fitaccen Mawakin Urhobo, Cif Daniel Iriferi Ya Rasu a Jihar Delta. Hoto: Daniel Iriferi.
Asali: Youtube

Yaushe mawakin ya rasu a jihar Delta?

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

The Nation ta tabbatar cewa marigayin ya fito ne daga yankin Abraka a karamar hukumar Ethiope ta Gabas da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin kafin rasuwarsa ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da yada aladun Urhobo a fadin kasar baki daya.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, iyalansa ba su fitar da sanarwa kan wannan babban rashi da aka yi ba, kamar yadda Punch ta tattaro.

An tabbatar da rasuwar jarumin fina-finan Nollywood

Har ila yau, kun ji cewa shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya, cewar Niger Delta Today.

Marigayin ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci a birnin Abeokuta a jihar Ogun.

An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne yayin da aka dauke shi daga kauyensu a karamar hukumar Remo zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

An tabbatar da cewa tun a watan Disambar 2023 Jimi ya ke ta yawo daga gida zuwa asibiti har zuwa wannan lokaci da ya ce ga garinku.

Fitaccen malamin addini ya rasu a Gombe

A baya, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci ya riga mu gidan gaskiya a Gombe bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Marigayin, Sheikh Muhammad Kobuwa ya rasu ne da safiyar ranar Juma'a 9 ga watan Faburairu a birnin Gombe.

Kafin rasuwarsa, Kobuwa shi ne Khalifan Darikar Tijjaniyya a jihar wanda ya ba da gudunmawa a bangarori da dama a koyarwar Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel