Bayan Barazanar da Suka Yi, Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Karin Alawus na 40% ga Ma’aikata

Bayan Barazanar da Suka Yi, Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Karin Alawus na 40% ga Ma’aikata

  • Bayan barazanar yajin aiki, gwamnatin tarayya ta amince da biyan sabon alawus na musamman ga ma’aikatan gwamnati a Najeriya
  • An ce sabon tsarin zai fara aiki daga 1 ga Mayu, 2026 domin rage radadin matsin tattalin arziki da yan Najeriya musamman ma'aikata ke fuskanta
  • Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta jaddada muhimmancin tattaunawa da gina amana tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta amince da biyan karin alawus na musamman na kashi 40 cikin 100 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya bayan matsin lamba da barazanar yajin aiki daga kungiyoyin kwadago.

Rahotanni sun nuna cewa an cimma matsayar ne bayan wani dogon zama da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Esther Walson-Jack, ta jagoranta ranar Talata a Abuja.

Shugabar ma'aikata.
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Esther Walson-Jack tana magana a wurin taro Hoto: Esther Walson-Jack
Source: Twitter

Ma'aikata za su samu alawus na 40%

Kara karanta wannan

An ware Naira Biliyan 1.4 domin saya wa Gwamna Ahmed Aliyu sababbin motocin aiki

Bussiness Day ta rahoto cewa a yayin taron, Hukumar Kula da Albashi da Kudin Shiga ta Kasa (NSIWC) ta fitar da takardar aiwatar da sabon alawus din.

Wannan lamarin ya kawo karshen kusan shekara biyu na koke-koken ma’aikata kan jinkirin da aka samu wajen daidaita albashi bayan amincewa da sabon mafi karancin albashi N70,000.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta jaddada muhimmancin tattaunawa da gina amana tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago domin kauce wa rikice-rikice da yajin aiki.

Ta ce duk da cewa kungiyoyin kwadago na da ‘yancin gabatar da bukatunsu, dole ne bangarorin gwamnati su samar da damar tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki.

Kungiyoyin kwadago sun yaba

Taron ya bai wa Majalisar hadin gwiwar kungiyoyin kwadago (JNPSNC) karkashin Benjamin Uyanto da shugaban NSIWC, Eyo Nta, damar gabatar da korafinsu kafin shugabar ma’aikatan gwamnati ta shiga tsakani domin samar da mafita.

Dukkan bangarorin sun yaba wa Esther Walson-Jack bisa rawar da ta taka wajen warware rikicin, kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Bayan tattaunawar, an gabatar da jadawalin aiwatar da sabon alawus na kashi 40 cikin 100 ga shugabannin JNPSNC.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27

Yan kwadago sun yi babbar nasara

Sakataren JNPSNC, Olowoyo Gbenga, ya bayyana matakin a matsayin babbar nasara ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

A cewarsa, sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayun 2026 bayan ma’aikata sun shafe lokaci tun daga watan Yulin 2024 suna jiran aiwatar da tsarin da ya danganci sabon mafi karancin albashi.

Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su rungumi tsarin domin ma’aikatan jihohi da kananan hukumomi su amfana.

Yan kwadago.
Yan kwadago yayin wata zanga-zanga da suka gudanar kan tsadar rayuwa a Najeriya Hoto; NLC HQ
Source: Getty Images

An dakatar da shirin yajin aiki

Olowoyo ya bayyana cewa kungiyar ta riga ta sanya ranar 21 ga watan Mayu domin fara yajin aikin kasa baki daya saboda jinkirin aiwatar da sabon tsarin.

Sai dai ya ce shiga tsakani da ofishin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya ya taimaka wajen shawo kan matsalar tare da dawo da kwarin gwiwar ma’aikata.

Yan Kwadago sun yi maganar karin albashi

A wani labarin, kun ji cewa kungiyoyin ƙwadago da suka hada da NLC da TUC sun ce za a fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya a watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta faɗi tarkon da ta ke yi wa tubabbun Boko Haram da Kur'ani

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce za a fara tattaunawa da wuri ne na da nufin tabbatar da cewa an kauce wa tsaiko da aka saba samu a tattaunawar albashi a baya.

Ya buƙaci ma’aikata da su haɗa kai domin neman albashi mai ma’ana.wanda ya dace da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262