Atiku Abubakar Ya Dauki Zafi, Ya Maida Martani kan Kalaman Babachir Lawal
- Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir lawal
- Atiku y ce Babachir na neman haddasa rabuwar kai tsakanin 'yan Najeriya, yana mai cewa bai kamata ya nun kabilanci ba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya musanta zargin cewa bai nuna damuwa ga wadanda hare-hare da tashe-tashen hankula suka shafa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya maida martani ga kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir David Lawal.
Atiku ya zargi Babachir da yin kalamai da ka iya rusa hadin kan da ke tsakanin 'yan Najeriya da kuma nuna bambancin kabila.

Source: Facebook
Atiku ya caccaki Babachir Lawal
Daily Trust ta ce martanin tsohon mataimakin shugaban kasar na kunshe a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi
Atiku ya ce abin takaici ne yadda Babachir ya zabi yin zarge-zarge da hasashe ba tare da gabatar da hujjojin da za su gaskata maganganunsa ba.
'Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce duk da dogon bayani da zarge-zargen da Babachir ya yi a kansa, bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da zarge-zargen da yake yi ba.
Atiku ya yi fatali da dorawa kabila laifi
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa abin da ya fi damunsa shi ne yadda Babachir ke kokarin alakanta wata kabila baki daya da aikata laifuffuka.
Ya ce abu ne mai hatsari da rashin adalci a dora wa wata kabila laifin wasu mutane saboda kawai suna da asali daya.
A cewarsa, idan aka bi irin wannan tunanin, za a iya dora wa kowace kabila laifukan da wasu tsiraru daga cikinta suka aikata, lamarin da zai iya haifar da rabuwar kai a kasa.
Abin da ya ba Atiku Abubakar mamaki
Atiku ya ce abin mamaki ne yadda Babachir ke sukar kabilar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga cikinta.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta yi magana kan sace Janar da matarsa, ta fadi kokarin da take yi
Ya tuna cewa Buhari ne ya nada Babachir a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, mafi girman mukamin da ya taba rike wa a gwamnati.
Ya ce:
"Babachir bai ki karbar mukami ko damar da ya samu daga shugaba Bahaushe-Fulani ba.
"Don haka yana da wahala a fahimci dalilin da ya sa yanzu yake kokarin bata sunan wata kabila saboda wani dan cikinta yana neman shugabancin kasa ta hanyar dimokuradiyya."

Source: Facebook
Yadda Atiku ya kare kansa daga zargi
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya musanta zargin cewa bai nuna damuwa ga wadanda hare-hare da tashe-tashen hankula suka shafa ba, kamar yadda Punch ta kawo.
Ya ce tsawon shekaru yana ci gaba da yin Allah-wadai da ta'addanci, garkuwa da mutane, rikice-rikicen kabilanci da addini da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.
Atiku ya soki Tinubu kan matsalar tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da sha'anin tsaro.
Atiku ya jaddada cewa tsarin tsaron ƙasar yana buƙatar sauyi cikin gaggawa domin magance barazanar tsaro da ke ƙara yaduwa a Najeriya.
Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta hanzarta gudanar da cikakkiyar bita kan tsarin manufofin yaƙi da ta'addanci na Najeriya.
Asali: Legit.ng
