Sabbabin Bayanai Sun Fito a kan Sace Ƙanwar Tsohon Minista Adelabu a Oyo

Sabbabin Bayanai Sun Fito a kan Sace Ƙanwar Tsohon Minista Adelabu a Oyo

  • ‘Yan sanda sun bayyana yadda masu garkuwa suka shafe makonni suna bibiyar dangin tsohon minista Adebayo Adelabu kafin sace ‘yar uwarsa da ‘ya’yanta
  • Bincike ya nuna masu laifin sun yi ƙoƙarin samun mai ba su bayanai daga cikin ma’aikatan gidan iyalan matar kafin a sace ta
  • Jami’an tsaro sun ceto matar da tagwayen ‘ya’yanta ba tare da sun ji rauni ba bayan farmakin da suka kai maboyar masu garkuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ibadan, jihar Oyo - Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta bayyana yadda wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane ta tsara tare da aiwatar da sace ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da tagwayen ‘ya’yanta maza.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Ayanlade Olayinka, ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa masu laifin sun shafe makonni suna bibiyar harkokin iyalan.

Kara karanta wannan

ADC na son raba Gawuna da Kwankwaso, an yi masa tayin takarar gwamnan Kano

Yadda aka gano shirin ƴan bindiga da suka sace yayar tsohon minista da yaranta
Yayar tsohon minista da yaranta kafin a sace su a hagu da yayanta, Adebayo Adelabu. Hoto: Ibadan mesi ogo
Source: Facebook

A wani rahoto da aka samu daga jaridar Premium Times, an ji miyagun sun shafe tsawon lokaci suna ta nazarin yadda za su dauke mutanen kafin kai harin.

Yadda aka sace ƴan uwan tsohon minista

A cewarsa, an sace Olaide Busayo Adegoke mai shekaru 42 da tagwayen ‘ya’yanta masu shekaru 11, Peter da Paul, a ranar 3 ga watan Yuni, 2026 yayin da take kai su makaranta.

Olayinka ya bayyana cewa wasu mutum huɗu dauke da makamai, waɗanda ke amfani da motar Toyota Corolla mai launin toka ba tare da rajista ba, sun tare su a titin Elewura da ke kusa da Ring Road a Ibadan da 7:30 na safe kafin su tafi da su.

Ya ce bincike ya tabbatar da cewa ba satar ɓakatatan ba ce, domin an shirya ta ne bayan dogon lokaci na sa ido da tattara bayanai kan iyalan.

An tara bayanai kan iyalan tsohon minista

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

Rundunar ta ƙara da cewa a watan Mayu, 2026 masu garkuwar sun yi yunƙurin samun haɗin kan wani ma’aikacin gidan da aka bayyana sunansa da Segun domin ya rika ba su bayanai daga cikin gida.

Bayan samun rahoton gaggawa kan lamarin, rundunar ta ce an fara tattara bayanan sirri nan take bisa umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda.

An kafa haɗin gwiwar jami’an sashen FID-IRT, rundunar Oyo da sauran ƙwararrun jami’an tsaro domin gano masu garkuwar da kuma ceto waɗanda aka sace.

Nasarar farko ta samu ne bayan kama wani wanda ake zargi mai suna Wale Abolalewa, wanda aka fi sani da “Oloro”, wanda tuni yake cikin jerin mutanen da ‘yan sanda ke sa ido a kansu.

Yan sanda sun ceto yayar Adelabu
Jami'an tsaro, yayar Adelabu, tagwayenta da wasu yan uwa bayan an ceto su Hoto: Ibadan mesi ogo
Source: Facebook

Bayanan da aka samu daga gare shi sun kai jami’ai ga wani babban wanda ake zargi mai suna Dare Oyedele, wanda aka fi sani da “Solution”, lamarin da ya taimaka wajen gano maboyar ƙungiyar a yankin Lado da ke Ayegun a Ibadan.

A ranar 6 ga Yuni da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, jami’an tsaro suka kai farmaki maboyar. A yayin farmakin, wani ɗan ƙungiyar mai suna Kelechi, wanda ya zo daga jihar Legas domin aikin, ya bude wa jami’an wuta.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

'Yan bindiga sun sace yayar tsohon minista

A baya, mun wallafa cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da yayar tsohon Ministan makamashi a Najeriya tare da tagwayen ‘ya ’yanta.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki lokacin da take kai ‘ya ’yanta makaranta, inda suka tafi da su da karfin tafiya zuwa maboyarsu.

Adelabu sun tabbatar da lamarin, sun nemi addu’a da taimakon jama’a, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike a kan batun, har ta kai ga an ceto su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng