Adelabu: Tsohon Ministan Tinubu Ya Tayar da Kura kan Zaben Fitar da Gwani na Gwamna

Adelabu: Tsohon Ministan Tinubu Ya Tayar da Kura kan Zaben Fitar da Gwani na Gwamna

  • Tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi magana kan zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Oyo
  • Adebayo Adelabu ya nuna cewa har yanzu uwar jam'iyya ta kasa ba ta sanar da sakamakon zaben ba a hukumance
  • Tsohon ministan ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar da ka da su fice daga cikinta inda ya nuna cewa hakan bai kamata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya aika sako ga mambobin jam'iyyar APC a jihar Oyo.

Adebayo Adelabu ya buƙaci mambobin APC da su kwantar da hankalinsu a daidai lokacin da ake cikin rashin tabbas game da sakamakon zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

Adelabu ya ce ba a sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na Oyo ba
Tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Duk da yana jam'iyyar adawa, Gwamnan Anambra ya manta da Obi ya ce a yi Tinubu

Me Adelabu ya ce kan zaben tsaida gwani?

Adelabu ya ce hedkwatar APC ta ƙasa ba ta bai ba wa kowane mutum, ƙungiya, ko kwamiti a jihar Oyo ikon sanar da sakamakon zaɓen fitar da gwanin ba.

Ya ce rahotannin da ke yawo a dandalin sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa game da 'yan takarar da suka yi nasara ya kamata a yi watsi da su, har sai lokacin da shugabancin jam'iyyar a Abuja ya fitar da sanarwa a hukumance.

“Sai dai kuma, yana da muhimmanci mu tunatar da kanmu cewa babban hedkwatar kasa ta jam'iyyar mu ta ba da umarni a sarari cewa babu wani mutum, ƙungiya, ko kwamiti a matakin jiha da ke da ikon sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓuɓɓukan fitar da gwani."
“Sakamakon haka, duk wani jerin sunayen 'yan takara da ake iƙirari ana yaɗawa a dandalin sada zumunta ko ta hanyoyin sadarwa da ba na hukuma ba ya kamata a yi takatsantsan da shi har sai shugabancin jam'iyyar na kasa ya fitar da sanarwarsa a hukumance.”

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta dakatar da dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa

- Adebayo Adelabu

Adebalu ya ba 'yan APC shawara

Adelabu ya yi kira ga mambobin jam'iyyar da magoya baya da su kasance masu haƙuri da bin doka da oda kamar yadda zancen ya zo a rahoton Punch.

Tsohon ministan ya kuma nuna damuwarsa game da rahotannin da ke cewa wasu mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa jam'iyyun adawa saboda yin amfani da tsarin maslaha.

Adelabu ya ba 'yan APC shawara
Adebayo Adelabu a wajen taron jam'iyyar APC Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Facebook
“Na damu ƙwarai da gaske da rahotannin cewa wasu daga cikin mambobinmu, waɗanda ke jin haushin jita-jitan da ke tattare da tsare-tsaren maslaha, sun fara sauya sheka zuwa jam'iyyun adawa domin nuna fushinsu."
“Bari na bayyana a fili ba tare da wata shakka ba cewa na yi tir da waɗannan sauya sheka baki ɗayansu.”

- Adebayo Adelabu

APC ta dakatar da dan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa ta dauki matakin ladabtarwa kan wani dan majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Hayatu Deen: Wanda ya fafata da Atiku a ADC ya yi maganar zuwa kotu kan sakamakon zaben

APC ta dakatar da 'dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim, daga jam’iyyar.

Ana zargin 'dan majalisar da wasu shugabannin APC a matakin mazaba da kananan hukumomi da aikata abubuwan da suka ci karo da manufofi da dokokin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng