Alkawarin da Aka Yi wa Tsohon Minista bayan Sace Yayarsa da Ƴaƴanta 2

Alkawarin da Aka Yi wa Tsohon Minista bayan Sace Yayarsa da Ƴaƴanta 2

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya nuna damuwa game da sace yayar tsohon minista a gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya
  • Makinde ya tabbatar wa tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, cewa gwamnati na kokarin ceto matar da 'ya'yanta biyu da aka sace
  • Gwamnan ya kai ziyarar jaje ga Adelabu da iyalansa domin nuna goyon baya tare da yi masa bayanin matakan da gwamnati ke dauka kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya sha alwashi kan rashin tsaro bayan sace yayar tsohon ministan makamashi.

Gwamnan ya tabbatar wa tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, cewa gwamnati za ta yi ƙoƙarin ceto ƴan uwansa.

Gwamna ya sha alwashin ceto yayar tsohon minista da aka sace
Yayar da tsohon minista da aka sace da ƴaƴanta, da Adebayo Adelabu. Hoto: Bayo Adelabu.
Source: Facebook

Makinde ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara gidan Adelabu domin yi masa jaje tare da nuna alhininsa kan sace ƙanwar tasa da yaran, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Gwamnan ya ce gwamnati na aiki tukuru domin ceto yayarsa da 'ya'yanta biyu da aka yi garkuwa da su.

Ta'addanci: Gwamna ya ziyarci tsohon minista

Makinde ya ce manufar ziyarar ita ce ya yi wa tsohon ministan bayani kan irin kokarin da gwamnati ke yi domin tabbatar da dawowarsu lafiya.

Ya bayyana cewa jami'an gwamnati da hukumomin tsaro suna ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da sauran matakan da suka dace domin gano inda suke.

Makinde ya shaida wa manema labarai cewa kowa ya san abin da ya faru da yayar Adelabu, wanda ya jawo damuwa ga iyalansa da al'umma.

Ya ce ya ga dacewar zuwa ya gana da Adelabu kai tsaye domin sanar da shi irin ci gaban da aka samu game da lamarin.

Gwamna ya yi magana bayan sace tsohon minista a Oyo
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ke Kudu maso Yamma. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Kokarin da gwamnati ke yi kan rashin tsaro

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an kubutar da matar da 'ya'yanta cikin koshin lafiya, cewar Daily Post.

A cewarsa, da yardar Ubangiji za a dawo da yayar Adelabu tare da 'ya'yanta gida, yana mai nuna kwarin gwiwa kan kokarin ceto su.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yadda aka yi yunkurin tayar da bam a gidan gwamnatin Ondo

Ya kuma bukaci jama'a su ci gaba da bai wa jami'an tsaro hadin kai tare da addu'o'i domin samun nasarar aikin ceton cikin gaggawa.

Lamarin sace dangin Adelabu ya jawo hankalin mutane da dama, yayin da iyalai da abokai ke ci gaba da fatan ganin an kubutar da su lafiya.

Ya kuma bukaci jama'a su ci gaba da bai wa jami'an tsaro hadin kai tare da addu'o'i domin samun nasarar aikin ceton cikin gaggawa.

An sace shugaban jam'iyyar Accord a Oyo

Mun kawo muku rahoton cewa 'yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar adawa a Osun yayin da jihar ke fama da hare-haren yan ta'adda.

Majiyoyi suka ce an kai shi asibiti domin ba shi kulawa, kuma likitoci sun tabbatar yana samun sauƙi sosai yayin jami'an tsaro suka bazama neman wadanda ake zargi da kai harin.

Rundunar 'yan sanda ta ce mahara biyu ne suka kai harin a kan babur yayin jami'ai suka fara farautar wadanda ake zargi tare da tabbatar da an fi da su a gaban kuliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.