"Suna Son Kashe Ni"; Babban Sarki Ya Hana Shan Barasa a Fadarsa
- Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya haramta Hennessy da sauran abubuwan sha masu maye a fadarsa
- Babban Sarkin a yankin Yarabawa ya ce barasa na da illa ga lafiya kuma na iya lalata wasu sassan jikin mutum
- Oba Akanbi ya ce duk wanda ya kawo masa Hennessy ko wani nau’in barasa yana son cutar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Iwo, Osun - Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya haramta Hennessy da sauran abubuwan sha masu maye a fadarsa, yana mai cewa suna da illa ga lafiya.
Sarkin gargajiya ya ce bai kamata a sake kawo masa ko wasu dattawa irin wadannan abubuwan sha ba.

Source: Facebook
Oba Akanbi ya sanar da matakin ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026.
Ya yi gargadin cewa duk wanda ya kawo abin sha mai maye zuwa fadarsa yana da niyyar “kawar da sarki.”
Oluwo ya yi gargadi
Oba Akanbi ya ce gin, schnapps da sauran nau’o’in barasa da ake warewa dattawa na da illa ga lafiya. Ya ce bai kamata a sake kawo su fadarsa ba.
“Abin da ake kira barasa da aka saba gabatarwa ko warewa dattawa na da illa ga lafiyarsu, kuma yana kaiwa ga mutuwa.”
“Duk wanda ya kawo abin sha mai zafi zuwa fadar sarki yana son kawar da sarki. Kada a kawo gin ko schnapps da ake warewa dattawa fadata, domin abin da ake kira barasar dattawa, Turawa ne suka kirkire ta domin kashe mutane da lalata gabobinsu na ciki.” In ji shi
Ya ce barasar na iya lalata koda har ta daina aiki.
Abin da Oluwo ya ce kan Hennessy
Oba Akanbi ya ce kwanan nan ya samu labarin cewa wasu baki sun kawo Hennessy fadarsa.
“Na ji kun kawo Hennessy, kada ku sake kawo ta nan. Kuna son kashe ni ne. Duk wanda ya kawo Hennessy ko wasu abubuwan sha masu maye masu hadari yana da niyyar kashe ni.”
Sarkin ya tambayi abin da zai yi da cikakkiyar kwalbar barasa, yana mai cewa:
“Idan na sha kwalba gaba daya, me zan yi da ita wajen yin addu’a?”
Barasa ba al’adar Yarbawa ba ce
Oba Akanbi ya ce barasa ba ta daga cikin al’adun kakannin Yarbawa. Masana lafiya sun dade suna gargadi kan illar yawan shan barasa, ciki har da cututtukan hanta da lalacewar koda.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce babu wani matakin shan barasa da za a iya cewa ba shi da hadari ga lafiya.

Source: Facebook
Sarkin ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa ake hana mata fita ko tafiya a wasu lokutan bukukuwan gargajiya.
Tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2016, Oluwo na Iwo ya sha sukar wasu al’adu da dabi’un gargajiya a yankin Yarbawa.
Oluwo ya ragargaji Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya yi Allah wadai da abun da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wa wasu sarakunan gargajiya a jihar Oyo.
Oluwo ya yi Allah wadai da abun da tsohon shugaban kasar ya yi sannan ya nemi wasikar ba da hakuri daga bangaren shi.
Asali: Legit.ng

