Da Gaske ’Yan Arewa Sun Shan Wuta da Tsada Fiye da ’Yan Kudu? Gaskiya Ta Fito
- 'Yan Najeriya da dama sun yada wani bidiyo da ke ikirarin cewa masu amfani da lantarki a Arewa suna biyan kudin wuta fiye da na Kudanci
- Binciken kwa-kwaf ya gano cewa hukumar NERC ne ke kayyade farashin lantarki bisa tsarin rukunan ba bisa yankin zama ba
- Rahoton ya bayyana cewa bambancin farashi yana da nasaba da irin rukunin da mai amfani yake ciki, ba Arewa da Kudu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A yan kwanakin nan, an fara ce-ce-ku-ce game da tsadar wutar lanatarki a Najeriya musamman Kudanci da Arewacin kasar.
Wani mai amfani da kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa masu amfani da lantarki a Arewacin Najeriya suna biyan kudin wuta da ya fi na Kudancin kasar yawa sosai.

Source: Getty Images
Rahoton da aka yada kan bambancin tsadar wuta

Kara karanta wannan
Sunday Igboho ya 'gano' manyan 'yan siyasa da ke daukar nauyin 'yan bindiga a Najeriya
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook a ranar 28 ga Mayu, 2026, mai ikirarin ya nuna hotunan sayen wutar lantarki daga Bauchi da Ibadan domin nuna bambancin farashi.
A cewarsa, Naira 1,000 a Bauchi ta sayi raka'o'in wuta hudu kacal, wanda ya kai Naira 250 kan kowace raka'a.
Ya kuma yi ikirarin cewa a Ibadan, Naira 90 ta sayi 'kilowatt' 8.5, wanda ya kai kusan Naira 10.59 kan kowane 'kilowatt'.
Daga wannan lissafi, ya ce Naira 1,000 za ta iya sayen kusan 'kilowatt' na wuta 94.4 a Ibadan, sabanin abin da ake samu a Bauchi.
Bidiyon ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu suka dauki lamarin a matsayin hujjar nuna wariya tsakanin yankunan Najeriya.
Gaskiyar ikirararin da ake yi
Sai dai binciken da Dubawa ta gudanar da bincike kan lamarin saboda yiwuwar yada bayanan da za su iya tayar da rikicin yanki da rashin fahimta.
Binciken ya nuna cewa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, ce ke kayyade farashin lantarki a fadin kasar baki daya.
A karkashin tsarin, ana raba kwastomomi zuwa rukunan 'Band' A, B, C, D da E gwargwadon sa'o'in wutar da suke samu kullum.
Masu 'Band' A suna samun akalla sa'o'i 20 na wuta a rana kuma suna biyan farashi mafi girma, yayin da sauran rukuni ke biyan kasa.
Rahoton ya duba jadawalin farashin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan, IBEDC, ya wallafa domin tabbatar da gaskiyar bayanan.

Source: Instagram
Binciken da aka yi kan farashi a JED
Bugu da kari, an tabbatar cewa tsarin farashin Kamfanin JED wanda ke samar da wuta a Bauchi da wasu jihohin Arewa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa kamfanin ma yana amfani da tsarin rukunan NERC iri daya wajen kayyade farashi ga kwastomomi.
Wannan na nufin mutane biyu a gari daya na iya biyan farashi mabambanta idan suna cikin rukunan sabis daban-daban.
Haka kuma, mutane daga yankuna daban-daban za su iya biyan farashi iri daya idan suna cikin rukuni guda na hukumar NERC.
Saboda haka, binciken ya bayyana cewa rade-radin cewa lantarki ya fi tsada a Arewacin Najeriya fiye da Kudanci karya ne.

Kara karanta wannan
Da gaske 'yan bindiga sun sako dalibai da malamai da suka sace a Oyo? Bayanai sun fito
Minista ya musanta gyara wuta a wata 6
Mun ba ku labarin cewa ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe ya yi karin haske kan yada wasu jita-jita game da gyaran wutar lantarki a kasar.
Ministan ya yana magana ne kan rahoton cewa ya yi alkawarin gyara matsalar lantarkin Najeriya cikin watanni uku yayin tantance shi.
Kakakinsa Adeola Adelabu ya ce Tegbe ya ce za a fara gyaran farko cikin kwanaki 100, amma manyan sauye-sauye za su dauki shekara guda.
Asali: Legit.ng
