Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifinsa Lahira bayan Yi Masa Dukan Kawo Wuka
- Abin al'ajabi ya faru a jihar Ondo bayan wani matashi ya yi wa mahaifinsa dukan tsiya har ya mutu
- ‘Yan sanda sun ce rikici ya barke tsakanin matashin da mahaifinsa mai shekaru 65, lamarin da ya kai ga mummunan hari da raunukan kai
- Kwamishinan ‘yan sanda Felix Ohagwu ya yi Allah wadai da lamarin, yana kira ga jama’a su kauce wa tashin hankali wajen warware sabani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Wani mutum mai shekaru 34 mai suna Nsikak Kingsley ya afka wa mahaifinsa tare da yi masa mummunan duka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukan kawo wuka da yaron ya yi ga mahaifinsa ya yi sanadiyar rasa ransa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Source: Twitter
Majiya daga The Nation ta ce lamarin ya faru ne a al’ummar Oda da ke karamar hukumar Akure ta Kudu, inda ya jawo damuwa da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Kara karanta wannan
Sunday Igboho ya 'gano' manyan 'yan siyasa da ke daukar nauyin 'yan bindiga a Najeriya
Yadda aka yi matashi ya kashe mahaifinsa
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mataimakin Sufetan ‘Yan Sanda Jimoh Abayomi, ya ce binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya samu sabani da mahaifinsa.
Abayomi ya bayyana cewa rikicin ya faru ne a ranar 28 ga Mayun 2026 tsakanin Nsikak Kingsley da mahaifinsa Adone Peter mai shekaru 65.
Ya ce sabanin ya rikide zuwa fada, inda aka yi zargin cewa mahaifin ya samu munanan raunuka a kansa yayin farmakin.
An garzaya da wanda aka kai wa harin zuwa cibiyar lafiya domin samun kulawa, amma daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Source: Original
Ana ci gaba da bincike kan matashin a Ondo
A cewarsa, an kama wanda ake zargin kuma yana tsare a hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, cewar Punch.
Ya kara da cewa an ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike da tantance musabbabin mutuwarsa.
Haka kuma an mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Abin da ya fusata kwamishinan yan sanda
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Felix Ohagwu, ya yi Allah wadai da abin da ya faru, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici kuma abin tir.
Ohagwu ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da adalci, tare da kira ga jama’a su guji tashin hankali wajen warware duk wata matsala.
Ya bukaci al’umma su rungumi hanyoyin zaman lafiya da bin doka wajen sasanta rikice-rikice, musamman wadanda suka shafi iyalai da zamantakewa.
Matashi ya hallaka mahaifinsa a Jigawai
A baya, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a Jigawa ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da daba wa mahaifinsa adda har ya mutu.
Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara, inda ake zargin matashin mai shekaru 20 ya kai wa mahaifinsa harin da ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya umarci a mayar da binciken lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID) da ke babban birni Dutse.
Asali: Legit.ng
