Zamfara: Ana Jita Jitar ba Malami Takara a ADC, Mahadi Ya Magantu kan Janye wa

Zamfara: Ana Jita Jitar ba Malami Takara a ADC, Mahadi Ya Magantu kan Janye wa

  • Ɗan takarar ADC a Zamfara ya yi magana kan jita-jitar cewa ya janye daga neman kujerar neman gwamna ƙarƙashin jam'iyyar
  • Mai magana da yawunsa, Salisu Mohamed Mada, ya bayyana cewa Mahadi ne halastaccen ɗan takarar ADC bayan ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani
  • Sanarwar ta zargi wasu masu siyasa da ƙirƙirar labarin ƙarya domin rikitar da jama'a, tare da gargadin cewa matakin na iya haifar da hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Dan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a Zamfara, Mahadi Aliyu Mohammed, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa kan takararsa.

Mahadi ya musanta rahotannin da ke cewa ya janye daga takararsa inda ya bayyana cewa yana nan daram.

Mahadi ya musanta labarin janye takarar gwamnan ADC
Dan takarar gwamnan ADC a Zamfara, Mahadi Aliyu Mohammed. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Salisu Mohamed Mada ya fitar a Gusau wanda jaridar Tribune ta samu.

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Babachir, sabuwar rigima ta bullo a ADC a jihar Adamawa

Mahadi ya magantu kan rade-radin janyewa daga takara

Mada ya bayyana cewa Mahadi Aliyu ne halastaccen ɗan takarar ADC na zaɓen gwamnan Zamfara na shekarar 2027.

Sanarwar ta ce hankalin Mahadi Aliyu Muhammad ya karkata kan wani rahoto na ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, wanda ke zargin cewa ya janye daga takararsa ta gwamna.

Ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, marar tushe kuma makirci da wasu matsanantan ’yan siyasa suka shirya domin yaudarar jama'a, haifar da ruɗani a siyasa da kuma tauye tsarin dimokuraɗiyya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, domin kauce wa shakku, Mahadi Aliyu ya shiga zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC, inda ya samu nasara kuma aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Dan takarar gwamna a ADC ya karyata rade-radin janye wa daga takara
Dan takarar jam'iyyar ADC a zaben gwamnan Zamfara mai zuwa, Mahadi Aliyu Mohammed. Hoto: Mahadi Aliyu Gusau
Source: Facebook

Gargaɗi da aka yi wa masu yada karya

Bayan samun nasarar, ya amince da amanar da mambobin jam’iyyar suka ɗora masa, kuma har yanzu shi ne sahihin dan takara, babu mai gardama kan matsayin ɗan takarar gwamna na ADC a Zamfara.

Kara karanta wannan

An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027

Sanarwar ta kuma yi gargadi ga waɗanda ke yaɗa wannan labari na bogi da su dakata nan take, tana mai cewa irin waɗannan ayyuka suna cutar da ƙimar dimokuraɗiyya da zaman lafiya.

A ƙarshe, ta gargadi cewa ci gaba da yaɗa irin waɗannan bayanan ƙarya na iya jawo matakan shari’a da hukunci da suka dace a kan masu hannu wajen aikata hakan wanda ba zai yi wa masu aikata hakan dadi ba, cewar Daily Post.

An yada jita-jitar ba malami takarar ADC

Mun ba ku labarin cewa wasu rahotanni sun fara yada jita-jitar cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta tsayar da Sheikh Abdulmudallib Muhammad takarar gwamnan Zamfara a 2027.

Duk da ba wata sanarwa a hukumance, an ce fitaccen malamin addinin musulunci ya samu tikiti bayan amincewar shugabanni da mambobin ADC.

Ana sa ran takararsa za ta kara zafafa fafatawar siyasa a jihar yayin da Gwamna Dauda Lawal ke neman tazarce a inuwar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.