Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi, Malam Abubakar Pharmacy Ya Rasu a Asibitin Kano
- Matashin malamin addinin musulunci a jihar Gombe, Malam Abbakar Sadiq Pharmacy ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a
- 'Dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe kuma tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pamtami ya tabbatar da rasuwar malamim
- Mutanen unguwar Pantami sun shaida wa Legit Hausa cewa malamin yana da kokari wajen karantarwa a masallacin Pharmacy
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - 'Daya daga cikin matasan malaman addinin musulunci a jihar Gombe, Malam Abubakar Sadiq, wanda aka fi sani da Abbakar Pharmacy ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rasu ne a wani asibiti da aka kwantar da shi jihar Kano bayan ya yi fama da jinya.

Source: Facebook
Tsohon ministan sadarwa kuma 'dan takarar gwamnan Gombe a inuwar PDP, Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da rasuwar Malam Abbakar a shafinsa na Facebook yau Juma'a.

Kara karanta wannan
Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"
Pantami ya tabbatar da rasuwar malamin
Pantami, wanda babban malamin musulunci ne a Najeriya ya yi alhinin rasuwar matashin malamin, tare da yi masa addu'ar samun rahama.
Sheikh Pantami ya ce:
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Allah Ya yi wa Malam Abbakar Pharmacy rasuwa a yau Juma'ah, bayan jinya da ya sha fama da ita.
"Muna roƙon Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa kabarinsa, Ya kuma bai wa iyalansa da masoyansa haƙuri da juriya.
"Allah Ya sa Aljannah ce makomarsa tare da iyayenmu da malamanmu da zurriyyarmu da aminanmu da yan'uwanmu,"
An fara jimamin rasuwar Malam Abbakar
Wani 'dan unguwar Pantami, Abubakar Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa marigayin ya sha fama da jinya tun a nan Gombe, kafin daga bisani a tafi da shi zuwa Kano.
Ya ce rasuwar Malam Abbakar babban rashi ne kasancewarsa da kokari matuka wajen yada addini da karantarwa a unguwar Pantami Yamma, musamman a masallacinsa da ake kira masallacin Pharmacy.

Source: Facebook
Ya ce:
"A wannan masallaci yake yawan karatuttukansa da mutane ke gani a kafafen sada zumunta, kuma yana da shagon saida magunguna na musulunci.
"Yana dan taba siyasa gaskiya, domin ko a bana,, ya nuna sha'awar neman kujerar dan Majalisar dokokin Gombe, mai wakiltar mazabar Gombe ta Kudu a 2027 amma sai rashin lafiya ya kama shi."
Mutumin ya kara da cewa a kwanakin baya bayan marigayin ya kwanta rashin lafiya, mutanen unguwa sun rika danganta ciwonsa da wata sarauta da aka ba shi a Bolari.
Sai dai ya ce jita-jitar mutane ce kawai, yana mai addu'ar Allah ya jikan Malam Abbakar Phramcy ya kuma masa rahama.
Malamin musulunci a Kwara ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin musulunci a Kwara, Ash-Sheikh Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya kasance kasance ɗa ga marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al-Adaby, wanda shi ne ya kafa gidauniyar Ansarul Islam Society of Nigeria.
Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kwara, Mai-Martaba Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari CFR, ya yi alhinin rasuwar malamin
Asali: Legit.ng

