An Rikita Oyo da Zanga Zanga kan Sace Dalibai da Bindiga Suna Makaranta
- 'Yan kungiyar fafutuka ta Take-It-Back suna zanga-zanga a yankin Mokola da ke birnin Ibadan kan tabarbarewar tsaro a jihar Oyo
- Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta ceto dalibai da malaman da aka sace a a jihar a kwanan nan
- Sun yi korafi da cewa sace-sacen jama’a na ƙaruwa a a fadin jihar, kuma yana shafar manoma, ’yan kasuwa, dalibai da sauran al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Mambobin ƙungiyar Take-It-Back sun gudanar da zanga-zanga shataletalen Mokola da ke Ibadan, jihar Oyo, kan tabarbarewar tsaro a jihar da kuma ci gaba da tsare ɗalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire.
Masu zanga-zangar, waɗanda suka taru a mashahuriyar mahadar da ke babban birnin jihar, sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an kubutar da waɗanda aka sace tare da dakile yawaitar sace-sace.

Source: Facebook
Kungiyar Take-It-Back ta wallafa wasu daga cikin hotunan mambobinta a lokacin da suke gabatar da zanga-zangar da safiyar yau Litinin 1 ga Yuni, 2026 a shafinta na X.
Kiran masu zanga-zanga a Oyo
Masu zanga-zangar na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce iri-iri suna nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin ƙaruwar rashin tsaro da ke shafar manoma, ’yan kasuwa da ɗalibai.
Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun haɗa da:
“A samar da tsaro ga kowa, ba ga wasu 'yan kaɗan ba,”
“Gwamnati ta kawo ƙarshen sace-sace a jihar Oyo,”
“Muna neman hanyoyi da al’ummomi masu aminci,”
“Ku kare manoma, ’yan kasuwa da ɗalibai,”
“Muna neman zaman lafiya, tsaro da adalci.”
Bayanin wani mai zanga zanga
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, ɗaya daga cikin matasan ya ce ’yan Najeriya na ƙara kosawa da matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar ƙasar.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Su sani cewa al’ummar Najeriya ba su cikin zaman lafiya. Su sani cewa al’ummar jihar Oyo ba su cikin walwala. Su sani cewa ’yan Najeriya sun gaji da rashin tsaro,”
Wannan zanga-zanga ta biyo bayan ƙarin fushi da aka nuna kan sace ɗalibai, dalibai da malamai a yayin hare-haren da aka kai makarantu a ƙauyen Ahoro-Esiele da ke karamar hukumar Oriire.

Source: Facebook
An sace waɗanda abin ya shafa ne lokacin da wasu ɗauke da makamai suka mamaye makarantu da ƙauyuka, lamarin da ya jawo damuwa sosai a tsakanin mazauna yankin da iyayen yara.
Bayanin wasu masu zanga zanga a bidiyo:
'Tinubu ya inganta tsaro,' APC
A wani labarin, kun ji cewa kakakin jam'iyyar APC na kasa, Felix Morka ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya inganta tsaro a Najeriya.
Morka ya ce yana ganin cewa babu wani shugaban kasa da ya yi aiki tukuru wajen magance matsalolin tsaro sama da Bola Ahmed Tinubu.
Maganganun da jagora a jam'iyya mai mulki ya yi sun zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da kai hare-hare da sace mutane a fadin kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

