Gwamnatin Tinubu Ta Nemo Mafita ga Al'ummar Najeriya kan Rashin Tsaro
- Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ba yan Najeriya shawara game da karuwar hare-hare
- Idris ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in tashin hankali a kasar
- Ya ce cin nasarar yaƙi da ta’addanci na buƙatar haɗin kan ƙasa baki ɗaya ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini, ƙabila ko yanki ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa al'umma cewa za ta ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo da Borno.
Gwamnatin ta ce wannan buri na daga cikin manyan abubuwan da ta bai wa fifiko a halin da ake ciki.

Source: Twitter
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka shirya domin tattauna halin tsaro da ƙasar, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci
Ta''addanci: Gwamnatin Tinubu ta shawarci yan Najeriya
Mohammed Idris, ya yi kira ga dukkan ’yan Najeriya da su shiga yaƙi da ta’addanci da sauran nau’o’in matsanancin tashin hankali da ke barazana ga zaman lafiya.
Idris ya bayyana cewa shawo kan matsalar ta’addanci yana buƙatar haɗin kai na ƙasa gaba ɗaya, wanda ya zarce bambance-bambancen siyasa, ƙabila, addini da yankuna daban-daban.
Ministan ya bayyana cewa hare-hare da sace mutane da ’yan ta’adda ke yi ba wai hari ne kan iyalai ko al’ummomi kaɗai ba, illa hari ne kan Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa dawo da ɗalibai da malamai da aka sace a hare-haren da suka faru a Oyo da Borno na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ke mayar da hankali.

Source: Twitter
Yadda ƴan Najeriya ke nuna juriya
A cewarsa, abubuwan da suka faru a Oyo da Borno sun sake gwada juriyar al’ummar Najeriya, yayin da sace yara da malamai ya zama babban barazana ga makomar ƙasa.
Ya ce sace ɗalibai da ba su san komai ba malamansu hari ne kan ilimi, makomar Najeriya da kuma haɗin kai da ke haɗa ’yan ƙasar wuri guda, cewar Tribune.
A cewarsa, ta’addanci ba ya da wata alaƙa da siyasa, kuma manufarsa guda ita ce haddasa ɓarna, tsoro da rashin zaman lafiya a cikin al’umma.
Idris ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da an ceto dukkan ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su.
Matsalar tsaro: Atiku ya dura kan Tinubu
An ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kan sace 'yar uwar Adebayo Adelabu da 'yan bindiga suka yi.
Atiku Abubakar ya koka da cewa matsalar rashin tsaro na kara tabarbarewa a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna cewa ana sanya 'yan Najeriya cikin zullumi da fargaba saboda rashin tsaro.
Asali: Legit.ng
