Umahi: Tinubu Ya Tattare Manyan Ayyukan Tituna a Arewa

Umahi: Tinubu Ya Tattare Manyan Ayyukan Tituna a Arewa

  • Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce kaso mafi tsoka na manyan ayyukan titunan gwamnatin Bola Tinubu suna Arewacin Najeriya
  • Umahi ya bayyana cewa rabon ayyukan ya nuna gwamnati na kokarin tabbatar da ci gaba mai daidaito a fadin kasa na don kai
  • Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce aikin babbar hanyar Gombe zuwa Biu zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da hada yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa yankin Arewa ne ke karbar mafi yawan manyan ayyukan titunan da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a kasar nan.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa yankin na da fiye da kashi 60 cikin 100 na ayyukan, yayin da Kudu ke da kusan kashi 40 cikin 100 na ayyukan tituna.

Kara karanta wannan

Gwamna Alia ya saukakawa manoma, za su samu taki a farashi mai rahusa

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin titi a Gombe
Ministan ayyuka David Umahi da gwamna Inuwa Yahaya, dukkaninsu sanye da hular aiki tare da sauran jami'a a Gombe Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya
Source: Facebook

A sakon da gwamna Inuwa Yahaya ya wallafa a shafin Facebook, an gano Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, 2026 yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Gombe.

Umahi ya magantu kan ayyukan Tinubu

Jaridar Punch ta ruwaito Umahi ya ce, rabon ayyukan ya nuna kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da ci gaba da bunkasa ababen more rayuwa cikin adalci a dukkan sassan Najeriya.

Ministan ya ce tsawon aikin titin daga Akwanga zuwa Maiduguri ya yi daidai da na babbar hanyar Lagos zuwa Calabar.

Ya jaddada cewa duk da yawancin ayyukan suna Arewa, ba Arewa kadai ke amfana da su ba, kamar yadda ayyukan da ke Kudu ba mutanen Kudun kadai ke amfani da su ba.

Umahi ya bukaci 'yan Najeriya su daina kallon ayyukan tituna a matsayin na yankuna daban-daban, yana mai cewa dukkanin jihohin kasar na cin gajiyar ayyukan hanyoyin Gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sabon nadi a gwamnatinsa, ya mika sunan ga majalisa

Umahi ya ce duka yan Najeriya na cin moriyar titunan da Tinubu ke gina wa
Ministan ayyuka na Najeriya, David Umahi Hoto: David Umahi
Source: Twitter

Gwamnan Gombe ya yabi Gwamnatin Tinubu

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana aikin hanyar Gombe zuwa Biu a matsayin wani babban ci gaba da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kara hadin kai tsakanin yankuna.

Ya ce aikin ya zo a lokacin da ake matukar bukatarsa, kuma zai taimaka wajen samar da karin damar kasuwanci da inganta rayuwar al'umma.

Gwamnan ya kuma yabawa gwamnatin jam'iyyar APC, yana mai cewa nasarorin da aka samu a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaba Tinubu sun zarce na gwamnatocin baya.

Gwamnatin Tinubu ta nemowa Najeriya mafita

A baya, mun kawo labarin cewa Ministan yaɗa labarai da wayar da kan ƴan ƙasa, Mohammed Idris, ya ba yan Najeriya shawara game da karuwar hare-hare.

Mohammed Idris ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in tashin hankali wanda ke hana kwanciyar hankali da nutsu wa a ƙasar.

Kara karanta wannan

Dan APC ya rasa mukaminsa saboda kiran Tinubu ya yi murabus daga kujerarsa

Ya ce cin nasarar yaƙi da ta’addanci na buƙatar haɗin kan ƙasa baki ɗaya ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini, ƙabila ko yanki ba yayin da ake samo mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng