Najeriya Ta Dauki Zafi, NUT Ta Shirya Zanga Zanga a Jihohi 36 kan Sace Dalibai a Oyo

Najeriya Ta Dauki Zafi, NUT Ta Shirya Zanga Zanga a Jihohi 36 kan Sace Dalibai a Oyo

  • An rufe makarantun firamare da sakandare na gwamnati a faɗin Jihar Oyo a ranar Litinin saboda sace dalibai da malamai da aka yi
  • A daya bangaren, malamai a fadin kasar nan sun bi umarnin Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) na fara zanga-zangar ƙasa baki ɗaya
  • Za su gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata domin nuna adawa da sace takwarorinsu da ɗalibai daga makarantu a Jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

jihar Oyo - A ranar 15 ga Mayu, 2026, wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari makarantu uku a ƙauyukan Esiele da Yawota na Ƙaramar Hukumar Oriire, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai.

Tun daga lokacin ne lamarin ya jawo Allah-wadai a faɗin ƙasar tare da zanga-zanga ana neman a ceto daliban daga hannun masu garkuwa da su.

Kara karanta wannan

An rikita Oyo da zanga zanga kan sace dalibai da bindiga suna makaranta

Lokacin da malamai suka yi zanga-zanga a Legas
Malamai na zanga-zanaga a Legas a 2014 kan sace dalibai a Chibok. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Binciken da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa an dakatar da harkokin karatu a makarantun gwamnati da ke ƙananan hukumomi 33 na Jihar Oyo sakamakon umarnin NUT.

Korafin malaman makaranta

Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa ya ce manufar zanga-zangar ita ce jawo hankali kan halin da malamai da ɗaliban da aka sace ke ciki.

Malamin ya ce:

“Tun ranar Lahadi bayan hutun Sallah na koma inda nake aiki a Ibarapa, sai ɗaya daga cikin shugabannina ya kira ni a waya ya sanar da ni cewa za a shiga yajin aiki ranar Litinin. Sai na dawo gida Ibadan domin bin umarnin.”

Wani malamin kuma ya ce:

“Wannan zanga-zanga ce ta nuna goyon baya ga malamai da ɗaliban da aka sace a Ahoro-Esienle. Ba za mu iya tunanin irin wahala da azabar da suke ciki a cikin kwanaki 18 da suka gabata ba.
"Muna roƙon gwamnatin tarayya da ta jihar da su gaggauta ɗaukar matakan ceto su.”

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

Malamai sun fara gangami

Ana sa ran malamai daga sassa daban-daban na ƙasar za su taru a gaban sakatariyoyin gwamnatocin jihohi a ranar Talata domin gudanar da zanga-zangar neman a saki malamai da ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo da sauran sassan ƙasar.

Za a gudanar da gangamin lokaci guda a manyan biranen jihohi 36 na ƙasar, wanda NUT ta shirya domin mayar da martani ga karuwar sace-sacen mutane da ke kai hari makarantu da ma’aikatan ilimi.

Matakin ya biyo bayan wata takarda da shugabancin ƙungiyar na ƙasa ya fitar a ranar 29 ga Mayu, 2026, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Audu Amba, da sakatarenta, Clinton Ikpitibo.

Takardar ta umarci rassan ƙungiyar na jihohi da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya domin jawo hankali ga matsalar rashin tsaro da ke addabar makarantu.

Wasu masu zanga zanga a Oyo
Yadda aka yi zanga-zangar adawa da sace dalibai a Oyo. Hoto: Take It Back Movement
Source: Facebook

Premium Times ta rahoto cewa a ranar Litinin ne aka fara isar da allunan zanga-zanga, tutoci da takardun wayar da kai zuwa sakatariyoyin NUT a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

'Idan na zama shugaban ƙasa,' Makinde ya fadi ayyukan da zai yi wa Najeriya

An kuma kammala shirye-shiryen samar da na’urorin ƙara sauti da motoci domin tallafa wa gangamin, yayin da ake sa ran hukumomin tsaro za su samar da kariya domin hana duk wata matsala.

An yi zanga-zanga a Oyo

A wani labarin, mun kawo muku cewa mabobin ƙungiyar farar hula ta Take-It-Back sun gudanar da zanga-zanga a safiyar Litinin a Mokola da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

'Yan kungiyar sun taru suna neman a ɗauki matakin gaggawa kan tabarbarewar tsaro a jihar da kuma ci gaba da tsare ɗalibai da malamai da aka sace daga Ƙaramar Hukumar Oriire.

Masu zanga-zangar sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Oyo da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace tare da magance matsalar sace-sacen mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng