An Bude Shafin Daukar Matasan Najeriya Aiki da Tallafin Kudi na ECOWAS

An Bude Shafin Daukar Matasan Najeriya Aiki da Tallafin Kudi na ECOWAS

  • ECOWAS ta buɗe shafin neman guraben shiga shirin horas da matasa na shekara guda ga ƴan Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka
  • Shirin zai bai wa waɗanda aka zaɓa damar yin aiki tare da hukumomin ECOWAS cikin cikakken tallafin kuɗi tare da samun horo da jagoranci
  • Masu sha'awar shiga shirin dole su kasance 'yan ƙasa membobin ECOWAS, ba su wuce shekara 32 ba, kuma su mallaki digiri daga jami'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta buɗe shafin neman guraben shiga shirin horas da matasa masu digiri na shekarar 2027 ga ƴan Najeriya da sauran ƙasashen da ke cikin ƙungiyar.

Shirin na shekara guda zai bai wa matasa damar yin aiki a hukumomi da cibiyoyin ECOWAS tare da samun cikakken tallafin kuɗi, horo da kuma gogewar aiki.

Kara karanta wannan

2027: Yadda Tinubu, Atiku da sauran ƴan takara ke shirin amfani da tsofaffin gwamnoni

Ofishin kungiyar ECOWAS
Mutane na hada-hada a ofishin kungiyar ECOWAS. Hoto: ECOWAS
Source: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa ECOWAS ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a ranar 31 ga Yulin 2026.

Waɗanda za su iya neman shirin

A cewar ECOWAS, masu neman shiga dole ne su kasance ƴan ƙasar da ke cikin ƙungiyar ECOWAS, ciki har da Najeriya.

Haka kuma, dole ne shekarunsu ba su wuce 32 ba tare da mallakar digiri a fannin da ya dace daga jami'a ko wata cibiyar ilimi da aka amince da ita.

An buɗe neman guraben ne daga ranar 31 ga Yulin 2026, yayin da za a rufe a ranar 31 ga Agustan 2026.

Bayani ga 'yan Najeriya

ECOWAS ta ce masu sha'awar shiga shirin su shiga shafin yanar gizon hukumar ta nan domin cike takardar neman gurbin shiga shirin.

Masu neman za su buɗe asusu, su cike bayanansu, su bayyana tarihin karatunsu da gogewar aikinsu sannan su ɗaura takardun da ake buƙata kamar takardar shaidar digiri, CV da wasiƙar bayyana dalilin neman gurbin.

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

Wajen taron kungiyar ECOWAS
Kashim Shettima na bayani a wani taron ECOWAS. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayan haka za su sake duba bayanan da suka shigar kafin su miƙa buƙatarsu.

Abubuwan da za a ba matasa

ECOWAS ta bayyana cewa waɗanda aka zaɓa za su yi aiki na tsawon shekara guda a hukumomi da cibiyoyin ƙungiyar kan ayyukan da suka shafi haɗin kan ƙasashen yammacin Afirka.

Shirin zai ba su damar samun gogewar aiki, ƙarin horo na musamman, jagoranci wajen bunƙasa ƙwarewa da kuma haɗuwa da ƙwararru daga yanki da ƙasashen duniya.

A cewar ECOWAS, manufar shirin ita ce samar da sababbin ƙwararrun matasa da za su taimaka wajen bunƙasa ci gaban yankin yammacin Afirka.

Tinubu ya ƙara albashin sojoji

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashin jami'an rundunar sojojin Najeriya da ke tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100.

Sabon tsarin zai amfani kusan jami'ai da dakaru 250,000, inda ake sa ran kuɗin albashin rundunar zai tashi daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924 a duk shekara.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta walwalar jami'an tsaro domin ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng