Zo Ku Nema: Gwamnatin Tarayya Ta Bude Shafin Daukar Sababbin Ma'aikata a NAQS
- Hukumar NAQS ta buɗe shafin ɗaukar ma'aikata, inda ta gayyaci ƴan Najeriya masu cancanta su nemi guraben aiki kafin Agusta 10, 2026
- Masu neman aiki za su cike fom a shafin NAQS, sannan waɗanda aka zaɓa za su rubuta jarabawar CBT tare da yin hira
- Hukumar ta gargadi masu neman aiki da su guji masu karɓar kuɗi, tana mai cewa aikin neman guraben gaba ɗaya kyauta ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja - Hukumar Kula da Killace Shuke-shuke da Dabbobi ta Najeriya (NAQS) ta buɗe ɗaukar sabbin ma'aikata, inda ta gayyaci ƴan Najeriya masu cancanta su nemi guraben aikin da ake da su.
An fara karɓar buƙatun neman aikin tun ranar 28 ga Yulin 2026, kuma za a rufe shafin neman aikin a ranar 10 ga Agustan 2026.

Source: Twitter
Abubuwan da za ka yi domin neman aikin
Hukumar Kula da Daidaito wajen Raba Mukamai (Federal Character Commission) ta tabbatar da hakan a shafinta na X, tana mai jaddada cewa neman aikin kyauta ne, kuma dole ne a cike fom ta shafin NAQS na yanar gizo.
Masu sha'awar neman aikin za su bi waɗannan matakai:
- Shiga shafin yanar gizon NAQS na ɗaukar ma'aikata.
- Buɗe sabon asusu ko shiga asusun da kake da shi.
- Zaɓi rukuni da matsayin aikin da kake son nema.
- Cika fom ɗin neman aiki da sahihan bayanan sirri da na karatu.
- Loda takardun shaidun da ake buƙata.
- Duba bayananka kafin ka tura buƙatar neman aikin.
Hukumar ta ce ba za a karɓi buƙatun da aka aika bayan wa'adin ƙarshe ba, haka kuma duk wanda bai bi ƙa'idar neman aikin ba za a soke buƙatarsa.
Guraben aikin da ake da su
An raba guraben aikin zuwa rukuni uku:
Superintendent Cadre
- Chief Superintendent of Quarantine Care
- Deputy Superintendent of Quarantine
- Assistant Superintendent of Quarantine II
Inspectorate Cadre
- Inspector of Quarantine I
- Inspector of Quarantine II
- Inspector of Quarantine III
Assistant Cadre
- Quarantine Assistant I
- Quarantine Assistant II
- Quarantine Assistant III
Sharuɗɗan cancanta da jadawali
Jaridar Punch ta rahoto cewa, masu neman aikin dole ne su kasance ƴan Najeriya, su mallaki lambar NIN, su kasance cikin ƙoshin lafiya, su kasance ba su da tarihin aikata laifi, sannan su cika sauran sharuɗɗan ilimi da na jiki da hukumar ta gindaya.

Source: Twitter
Hukumar ta ce:
- Za a rufe neman aiki ranar 10 ga Agusta, 2026.
- Za a fitar da sunayen waɗanda suka yi nasara ranar 13 ga Agusta, 2026.
- Za a gudanar da jarabawar CBT da hira ranar 15 ga Agusta, 2026.
NAQS ta gargadi masu neman aiki da kada su biya kuɗi ga kowa, tana mai jaddada cewa dukkan tsarin ɗaukar ma'aikatan kyauta ne, kuma ya kamata su dogara da shafin hukuma kawai domin samun sahihan bayanai.
Haramta safarar fatar jaki a Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen ketare inda ake amfani da su wurin magunguna da wasu abubuwan.
Shugaban hukumar NAQS ne ya fitar da sanarwar a matsayin martani kan rahoton da aka fitar kan kuskure na cewa an dage haramcin.
Gwamnatin tarayyar ta saka haramci ne kan safarar fatar jakan saboda adadin jakunan da ake da su a Najeriya sun tasan ma karewa.
Asali: Legit.ng


