An Kwarfe na Hannun Daman Trump Mai Adawa da Musulmi a Zaben Amurka

An Kwarfe na Hannun Daman Trump Mai Adawa da Musulmi a Zaben Amurka

  • Dan majalisar dokokin Amurka, Andy Ogles, wanda ya yi kaurin suna wajen furta kalaman adawa da Musulmi, ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Republican a jihar Tennessee
  • Ogles ya sha kaye ne a ranar Alhamis a hannun tsohon kwamishinan noma na jihar, Charlie Hatcher, duk da goyon bayan Donald Trump da Ogles y samu kafin gudanar da zaben
  • Hatcher ya samu kashi 53.3 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Ogles ya samu kashi 46.8 cikin 100, kamar yadda rahotanni suka bayyana bayan an kirga kashi 95 cikin 100 na kuri'un

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nashville, Amurka – Dan majalisar wakilan Amurka, Andy Ogles, ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Republican a jihar Tennessee, inda Charlie Hatcher ya doke shi duk da cewa Shugaba Donald Trump ya goyi bayan shi.

Kara karanta wannan

'Kuri'u 16 ka samu': Davido da Bashir Ahmad sun kaure da faɗa, sun ƙunyata juna

Ogles, wanda aka fara zabe shi zuwa majalisar wakilai a shekarar 2022, ya fuskanci Hatcher, tsohon kwamishinan noma na Tennessee, a zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Alhamis.

Andy Ogles da ya sha kaye
Dan majalisar Amurka da aka kwarfe, Andy Ogles. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta rahoto cewa Hatcher ya samu kashi 53.3 cikin 100 na kuri'un, yayin da Ogles ya samu kashi 46.8 cikin 100 bayan an samu sakamakon kashi 95 cikin 100 na mazabu.

Trump ya goyi bayan Ogles

Kashin bayan Ogles ya zo ne duk da cewa DonaldTrump ya nuna masa cikakken goyon baya a ranar da aka gudanar da zaben.

Trump ya bayyana Ogles a matsayin dan takarar da yake ba shi "cikakken goyon baya", amma hakan bai hana Hatcher samun nasara ba.

Hatcher shi ma ya bayyana kansa a matsayin mai goyon bayan Trump, kuma Gwamnan Tennessee, Bill Lee, ya ba shi goyon baya a karshen yakin neman zaben fitar da gwani.

An soki kalaman Ogles kan Musulmi

Ogles, wanda yake daga cikin masu tsananin goyon bayan Isra'ila, ya sha fuskantar suka daga bangarori daban-daban saboda kalaman da ya yi kan al'ummar Musulmi.

A watan Maris, ya wallafa wani sako yana cewa Musulmi ba su cikin wadanda ya kamata su kasance a cikin 'yan Amurka, tare da sukar tsarin zaman tare na addinai daban-daban.

Kara karanta wannan

Siyasar Amurka: Abdul El Sayed ya gaza hakuri, ya yi wa Trump zazzafan martani

Hatcher ya taba yin watsi da irin wannan matsaya ta Ogles, yana mai cewa akwai Musulman da suke 'yan Amurka masu bin doka, sannan akwai Musulman da ke aikin soja a rundunar Amurka.

Hatcher zai fafata a zabe

Bayan nasarar da ya samu, Hatcher zai wakilci jam'iyyar Republican a babban zaben watan Nuwamba, inda zai fafata da Chaz Molder, magajin garin Columbia na jam'iyyar Democrat.

Molder ya lashe zaben fidda gwani na Democrat da kashi 40.9 cikin 100 na kuri'un da aka kada a cikin zaben da 'yan takara da dama suka fafata.

Gundumar da Hatcher zai wakilta ta karkata sosai ga jam'iyyar Republican, yayin da 'yan Democrat ke kokarin amfani da damuwar jama'a kan tattalin arziki da yakin Iran wajen samun kujerun jam'iyyar Republican a zaben.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Anadolu ta wallafa cewa Ogles ya zama dan takara na biyu da Trump ya goyi baya da ya sha kaye a zaben fidda gwani cikin wannan makon.

A ranar Talata, Amir Hassan, tsohon sojan ruwa da Trump ya goyi baya a Michigan, shi ma ya sha kaye a hannun Thomas Smith, duk da cewa Smith ya dakatar da yakin neman zabensa kafin gudanar da zaben.

Kara karanta wannan

Adeleke ya zargi EFCC da shirin yi wa gwamnatinsa illa gabanin zaɓen Osun

Ga bidiyon Trump yana masa kamfen da Ogles ya wallafa a X:

Abdul El-Sayed ya ci zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdul El-Sayed ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat na kujerar Sanata a Michigan.

Nasarar ta sanya El-Sayed, dan Democrat mai ra'ayin siyasa mai sassauci, fuskantar tsohon dan majalisar wakilai na Republican, Mike Rogers

Jam'iyyar Democrat ta yi gaggawar nuna hadin kai bayan nasarar El-Sayed, inda Stevens ta yi alkawarin taimaka masa wajen doke Rogers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng