Hukumar Hisbah Ta Kama Musulman da Ke Cin Abinci a Bainar Jama’a Ana Azumi

Hukumar Hisbah Ta Kama Musulman da Ke Cin Abinci a Bainar Jama’a Ana Azumi

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wasu Musulmai 11 da ke cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin watan Ramadan
  • Hisbah ta kama mutanen ne bayan da ta gudanar da bincike a gidajen cin abinci da kasuwanni kamar yadda ta saba yi duk shekara
  • Kafin hukumar ta sake su, wadanda aka kaman, maza 10 da mace daya, sun yi rantsuwa kan cewa ba za su sake aikata hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kama wasu musulmi 11 a ranar Talata wadanda aka gansu suna cin abinci da rana a lokacin azumin watan Ramadan.

Musulmi su ne mafi rinjaye a al'ummar jihar Kano kuma jihar na bin tsarin shari'ar Musulunci sau da kafa wanda hakan ne ma ta sa aka kama mutanen.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Hisbah ta aika da muhimmin gargadi ga wadanda ba musulmai ba a Kano

Ramadan: Hisba ta kama Musulmai a Kano
Hisbah ta kama Musulma 11 suna kwasar girki ana tsaka da azumi a Kano. Hoto: Hisbah Board Kano
Asali: Facebook

Hisbah ta kama mutanen ne bayan da ta gudanar da bincike a gidajen cin abinci da kasuwanni kamar yadda ta saba yi duk shekara a cikin watan Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa hukumar ta saki mutanen 11 (maza 10 da mace daya) bayan sun yi rantsuwa cewa ba za su sake cin abinci a bainar jama'a alhalin ana yin azumi ba.

Za a kama wadanda ba Musulmai ba?

Kakakin hukumar Hisbah na Kano, Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa:

"Mun kama mutane 11 a ranar Talata ciki har da wata budurwa mai sayar da gyada da aka ga tana cin gyadar a bainar jama'a, wasu mutane suka kai mana rahoto."
“Sauran 10 din maza ne kuma an kama su a sassa daban-daban na birnin jihar musamman kusa da kasuwannin da ake yawan hada-hada."

Kara karanta wannan

Ramadan 2024: Wane lokaci ne ake gama sahur? Fitaccen malami ya ba da amsa

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike amma ya ce an kebe wadanda ba musulmi ba daga wadanda za a kama.

"Zamu kama wadanda ba musulmi ba ne kawai idan muka gano cewa suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata a ce suna yin azumi."

- A cewar Lawal Fagge.

Hisbah ta gargadi wadanda ba Musulmi ba

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, hukumar Hisbah ta Kano ta gargadi wadanda ba Musuli ba a jihar da kada su rinka cin abinci a fili ko kuma su yi wani abu da zai gurgunta addinin Musulunci.

Darakta Janar na hukumar, Abba Sai’Idu ya ce jami'an hukumar za su tsaurara sintiri a cikin gari domin kame duk wani musulmi da aka gani yana aikata wani aiki da bai dace da al’adar Musulunci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel