Amnesty: 'Yan Bindiga na Korar Mutane a Gidajensu ana Rububin Sallah

Amnesty: 'Yan Bindiga na Korar Mutane a Gidajensu ana Rububin Sallah

  • Kungiyar Amnesty International da ke rajin kare hakkin dan Adam ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan ta dukufa wajen kare rayukan al'ummar kasar
  • Amnesty ta yi korafi da cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane na cigaba cin karen su babu babbaka a wasu kananan hukumomin jihar Sokoto
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi martani kan korafin da kungiyar Amnesty ta yi, inda wasu suka jingina lamarin da siyasa da zaben shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Kungiyar Amnesty International ya yi korafi kan yadda 'yan ta'adda ke cigaba da fatattakar mutane a gidajen su a Sokoto.

Kungiyar kare hakkin dan Adam din ta ce masu garkuwa da mutane sun saka jama'a a gaba a wasu kananan hukumomin jihar, musamman a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi barazana ga masu alakanta shi da goyon bayan 'yan bindiga

'Yan gudun hijira a Sokoto
Mutanen da suka rasa muhalli saboda rashin tsaro a Sokoto. Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Amnesty International ta yi magana da kakkausar murya kan rashin tsaro ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Maganar Amnesty kan rashin tsaro

Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen kare rayuka da duniyoyin al'umma, musamman a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa a jihar Sokoto.

Amnesty ta alaƙanta ƙaruwar korar mutane daga gidajen su da 'yan ta'adda ke yi da gazawar hukumomi, inda ta ce ba za a yarda da hakan ba.

Cikakken sakon da kungiyar ta wallafa ya ce:

"Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da gazawar hukumomin Najeriya wajen kare rayuka yayin da ‘yan bindiga ke kara kai hare-hare a kauyuka daban-daban da ke cikin kananan hukumomin Isa da Sabon Birni na jihar Sokoto.
"Daga jiya zuwa yau an kori mutane daga kauyukansu, an yi garkuwa da mutane yayin da har yanzu ba a san inda mutane da dama suke ba."

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke tsohuwa mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Da ta ke kira ga gwamnati, Amnesty ta ce:

"Gwamnati na da alhakin kare al’ummarta. Karuwar mace-mace, garkuwa da mutane da kuma raba jama’a da muhallansu a Arewacin Najeriya na nuna yadda hukumomi suka gaza wajen sauke wannan nauyi."
Yan gudun hijira a Sokoto
Mutanen da 'yan bindiga suka kora a gidajen su a Sokoto. Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

Martanin 'yan Najeriya kan korafin

'Yan Najeriya da dama sun yi magana kan korafin da kungiyar Amnesty ta yi, inda wasu daga ciki suka ce lamarin na bukatar kulawa ta musamman.

Ahmad Jaagi ya ce:

“Kuma har yanzu wasu suna son mu sake zaben Tinubu da APC. Tambayata ita ce, domin (Tinubu) ya dawo ya yi me?”

Muhammad Tasi'u Hassan ya ce:

“A wannan lokaci har yanzu wasu suna son mu zabi gwamnatin APC, suna tunanin muna kama da su ne. Mu ba kamar sauran magoya bayan APC ba ne.”

Rohmah ta ce:

“Ci gaba da gazawar kare rayuka da dukiyoyi a Najeriya ya nuna karara cewa tsarin da ake kai yanzu ya gaza.”

Boko Haram na barazanar kai hari

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta samu rahoto kan harin da Boko Haram ke son kai wa.

Dakarun Operation Hadin Kai ne suka bayyana cewa 'yan ta'addan sun shirya kai hare-haren kunar baƙin wake a lokacin bikin babbar sallah a Arewa maso Gabas.

Sai dai sojojin sun karfafi jama'ar yankin da cewa sun shirya tsaf domin magance duk wata barazana da kungiyar Boko Haram za ta haifar a lokacin sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng