Alkawura 6 da Ƴan Siyasar Najeriya Suka Gaza Cikawa tun Dawowar Dimukradiyya
Ƴan siyasar Najeriya sun dade suna yin alƙawuran magance matsalolin da ke damun kasar tun bayan samun 'yancin kanta wanda har zuwa yanzu ba a cikawa su ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tun bayan dawowar tsarin dimokraɗiyya a shekarar 1999, shugabannin Najeriya daban-daban sun yi ta yin alƙawuran gyara rayuwar al’umma.
Duk da sauyin gwamnati daga lokaci zuwa lokaci, har yanzu wasu manyan matsaloli suna ci gaba da addabar ƙasar.

Source: Twitter
Manyan alkawura da aka gaza cikawa a Najeriya
A yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, an sake fara jin irin waɗannan alƙawura daga bakin ƴan siyasa, cewar rahoton BBC Hausa.
Masanin siyasa a jami’ar Namibia, Farfesa Babayo Sule, ya ce ƴan siyasa sun fahimci irin matsalolin da suka fi damun jama’a, don haka suke amfani da su wajen neman goyon bayan masu zaɓe.
Ya bayyana cewa galibi suna sukar waɗanda ke mulki tare da alƙawarin za su yi abin da suka kasa yi idan suka samu dama.
Legit Hausa ta yi duba game da wasu manyan bangarori da Babayo Sule ya ce an dade ana fama da matsaloli ba tare da ɗaukar mataki ba.
1. Wutar lantarki
Matsalar wutar lantarki ta daɗe tana addabar Najeriya duk da kuɗaɗen da aka kashe domin inganta fannin.
An yi gyare-gyare da dama ciki har da sauya tsarin mallakar kamfanonin lantarki, amma har yanzu mutane da kamfanoni suna dogaro da janareto domin gudanar da harkokinsu.
Masana sun ce rashin wadatacciyar lantarki na jawo babbar asara ga tattalin arzikin ƙasar.
Duk da alƙawuran shugabanni da dama, har yanzu yawan wutar da ake samarwa bai kai buƙatar al’umma ba.

Source: Instagram
2. Bangaren Ilimi
Bangaren ilimi na fuskantar matsaloli masu yawa duk da alƙawuran da gwamnatoci ke yi na inganta shi.
Adadin yaran da ba su zuwa makaranta yana ci gaba da ƙaruwa, musamman a yankunan karkara da ke fama da ƙarancin makarantu da kayan koyarwa.

Kara karanta wannan
'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki
Haka kuma kaso da gwamnati ke warewa ilimi a kasafin kuɗi bai kai matakin da ƙungiyoyin duniya ke ba da shawara ba, lamarin da ke hana samun ci gaba mai dorewa.
3. Harkar tsaro
Matsalar tsaro na daga cikin manyan ƙalubalen da suka daɗe suna damun Najeriya kama daga ta'addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane.
Ƴan siyasa kan yi alƙawarin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuka, amma har yanzu ana fama da hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar.
Rikice-rikice sun jawo asarar rayuka da dukiyoyi tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu, cewar Premium Times.
Duk da ƙoƙarin gwamnatoci daban-daban, hare-haren ƴan ta’adda da sauran ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Source: Facebook
4. Yaƙi da cin hanci
Kusan kowace gwamnati ta yi alƙawarin yaƙar cin hanci da rashawa tare da tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati.
An kafa hukumomi da dama domin yaƙar wannan matsala tare da gurfanar da wasu mutane a gaban kotu.
Sai dai duk da waɗannan matakai, masana suna ganin har yanzu cin hanci da rashawa na ci gaba da zama babban ƙalubale.
Ana ci gaba da samun rahotannin zargin almundahanar kuɗaɗen jama’a da kuma karkatar da dukiyoyin gwamnati.
5. Inganta hanyoyi
Najeriya na da babbar hanyar hada tituna a Afirka ta Yamma, amma yawancin hanyoyin suna cikin mummunan yanayi.
Hakan na haddasa yawaitar haɗura da asarar rayuka a da ake yawan samu a sassa daban-daban na ƙasar.
Shugabanni da ƴan takara kan yi alƙawarin gina sababbin hanyoyi ko gyara tsofaffi domin samun goyon bayan jama’a.
Duk da haka, har yanzu akwai wurare da dama da ke fama da rashin ingantattun hanyoyin sufuri.

Source: Twitter
6. Kiwon lafiya
Bangaren lafiya ma na daga cikin wuraren da ƴan siyasa suka fi yawan yin alƙawarin gyarawa, kamar yadda Punch ta ce.
Asibitoci da dama na fama da ƙarancin kayan aiki, magunguna da ma’aikatan lafiya da ake buƙata domin kula da marasa lafiya yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa mace-macen yara da mata masu juna biyu na ci gaba da zama babbar matsala.
A lokaci guda, wasu shugabanni da masu kuɗi kan je ƙasashen waje neman magani, yayin da talakawa ke amfani da asibitocin cikin gida masu fama da matsaloli.
'Yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga durkushewa'
A wani labarin, kun ji cewa Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya bayyana kokarin Bola Tinubu ya yi wurin ceto Najeriya.
Hadimin shugaban kasar ya ce Bola Tinubu ya “sadaukar da komai” domin ceton Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki da tabewa.
Ya ce sauye-sauyen Tinubu kamar cire tallafin mai da daidaita darajar naira sun taimaka wajen ƙara kuɗin jihohi da ayyukan ci gaba.
Asali: Legit.ng


