Jihohin Arewa 3 da Suka Fi Yawan Yaran da ba Su zuwa Makaranta, Jigawa ce a gaba

Jihohin Arewa 3 da Suka Fi Yawan Yaran da ba Su zuwa Makaranta, Jigawa ce a gaba

  • Hukumar UNICEF ta bayyana cewa jihohin Jigawa, Kano, da Katsina ne sahun gaba a yawan yaran da ba su zuwa makarantar zamani ta boko
  • Najeriya ce ke da mafi yawan yara marasa zuwa makaranta a duniya, inda adadinsu ya kai miliyan 18.3, kamar yadda hukumar ta bayyana
  • Masaniyar ilimi ta UNICEF, Aisha Abdullahi, ta bayyana cewa talauci, rashin tsaro ne ke rura wutar wannan matsala, inda ta kuma kawo mafita

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano – A wani taron tattaunawa da aka yi da ƴan jarida, hukumar UNICEF ta nuna cewa jihohin Jigawa, Kano, da Katsina ne a sahun gaba a yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Hukumar UNICEF ta yi nuni da cewa Jigawa, Kano da Katsine kaɗai suna bayar da gudunmawar kusan kashi 30 cikin ɗari na yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya.

Kara karanta wannan

INEC ta shirya yin zabe a Kano da wasu jihohi 5 a watan Yuni

UNICEF ta jero jihohin Arewa 3 da suka fi ko ina yawan yara marasa zuwa makaranta.
Daliban sakandare sun yi sahu a Ibafo, jihar Ogun. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Matsalar ilimin yara a Arewacin Najeriya

Masaniyar ilimi ta hukumar, Aisha Abdullahi, ta bayyana cewa talauci, rashin tsaro, da al'ada ne ke rura wutar wannan rikicin ilimi a Arewa, in ji rahoton The Nation.

Aisha Abdullahi ta jaddada cewa:

“Ilimin yara daga firamare ba wai iya sharar fage yake yi ba, har ma yana zama mataki na musamman na rage yawan yara marasa zuwa makaranta.”

Aisha ta ce kusan kashi 90 cikin 100 na haɓakar ƙwaƙwalwa yana faruwa ne kafin yaro ya kai shekaru biyar, wanda hakan ya sa wannan lokacin ya zama mafi mahimmanci ga ilimantar da yara.

Haka kuma, wannan tsari yana taimakawa wajen kare ƴaƴa mata daga matsin lambar auren wuri ta hanyar sanya su cikin tsarin ilimi tun da wuri.

Gudunmawar iyaye maza

Masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan yadda kashi 15 kawai na iyaye maza ke shiga harkokin ilimin yaran na farko a yankin Arewa, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karyata jita jita, ya jero ayyukan da gwamnatinsa ke yi a yankin Arewa

Ana sa ran cewa idan iyaye maza suka ƙara shiga cikin lamarin, hakan na iya rage yawan yaran da ke daina zuwa makaranta da kashi 50.

Wannan ya biyo bayan tasirin da uba ke da shi wajen yanke shawara a cikin gida, wanda ke da matuƙar mahimmanci ga makomar yara.

Don haka, UNICEF ta ba da shawarar yin amfani da masallatai da shirye-shiryen tuntuɓar al'umma domin ƙarfafa maza wajen ba da fifiko ga ilimin ƴaƴansu.

UNICEF ta ce shekara daya zuwa 5 ne lokacin da yaro ya fi kwankwadar ilimin da zai saita tafiyar iliminsa har zuwa girma.
Wani yaro ya na rubutu a kan allo a cikin ajin makarantar boko. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ƙalubalen yankunan karkara

Duk da cewa jihohi da dama sun ayyana ilimin firamare da na sakandare kyauta, har yanzu akwai ƙarancin zuwan yara makarantu a ƙauyuka.

Hukumar UNICEF ta yi kira da a sauya salon aiwatar da wannan shiri, gwamnatoci su zuba jari sosai wajen inganta tsarin koyarwa da kuma gina makomar yaran da suka kammala karatu don jan ra'ayin 'yan baya.

Aisha ta buga misali da cewa, wuraren da ke samar da ilimi masu cibiyoyin ECCDE sun samu kusan kashi 40 na yawan karuwar sanya yara ajin farko na makarantar firamare, da kuma dorewar zuwansu makaranta.

Kano ta cika sharadin inganta ilimi

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwa yau Laraba, NiMet ta hango matsala a Kano da wasu jihohin Arewa

A wani labari, mun ruwaito cewa, jihar Kano ta kere sauran jihohi da ke Arewa maso Yamma bayan ta cika ka’idar 26% na kasafin ilimi a shekarar 2026 a shiyyar.

Kano ta zama ita kaɗai ce ta cika sharaɗin a yankin da ke fama da karuwar yara marasa zuwa makaranta da masu gararamba a tituna.

Jihohin Jigawa da Katsina sun yi fice wajen zuba kudi da gyaran tsarin karatun tsangaya duk da an fuskanci kalubale a wajen aiwatar da kasafin 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com