An Samu Sababbin Bayanai kan Yadda Aka Sace Shugaban Karamar Hukuma a Zamfara

An Samu Sababbin Bayanai kan Yadda Aka Sace Shugaban Karamar Hukuma a Zamfara

  • Iyalan shugaban karamar hukumar Bungudu sun yi magana game da yadda 'yan bindiga suka sace dan siyasar a Zamfara
  • Wani da aka saki ya ce maharan sun zo da cikakken bayanin dan siyasar, lamarin da ya nuna sun shirya harin tun kafin kaiwa
  • Iyalan sun zargi jami'an tsaro da jinkirin kai dauki, suna cewa da an gaggauta amsa kiran neman agaji da ba a yi garkuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bungudu, Zamfara - Iyalan shugaban karamar hukumar Bungudu a Jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, sun bayyana yadda 'yan bindiga suka sace shi.

Sun ce maharan sun mamaye gidansa na kusan sa'o'i biyu kafin su yi garkuwa da shi ba tare da fargaba ba.

Yadda aka sace shugaban karamar hukuma
Shugaban karamar hukumar Bungudu a Zamfara, Nura Umar Abdullahi. Hoto: Mashkur Yahaya Bug.
Source: Facebook

Yadda aka sace shugaban karamar hukuma

Sun ce maharan dauke da makamai sun kashe jami'an tsaro biyu, wani dan banga da mai sayar da ruwa kafin su tsere da shugaban karamar hukumar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda daliban Jami’ar Jos suka hallaka matashi kan zargin sata wayar iPhone

Abdulssalam Yunusa Mai Jama'a, wanda aka yi garkuwa da shi amma aka sake shi daga baya, ya ce maharan sun zo da cikakken bayani kan motsin shugaban.

Ya ce sun shigo dakinsa suna tambayar ko shugaban yana gida, sannan suka nace cewa sun san ya dawo tare da wasu mutane uku.

Yunusa ya bayyana cewa maharan kimanin mutum 20 ne, kuma sun fara kokarin karya kofofi uku kafin daga bisani su samu hanyar shiga gidan.

Ya ce sun daure hannuwansa tare da tsare shi a bayan gida, kafin daga baya su fito da matar shugaban karamar hukumar da 'yarsa da kuma shi dan siyasar.

A cewarsa, shugaban ya roki maharan su saki iyalansa su tafi da shi kadai, yana mai alkawarin ba su duk abin da suke bukata.

Yan bindiga sun sace ciyaman a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An sake iyalan shugaban karamar hukuma

Daga bisani, maharan sun saki iyalansa amma suka tafi da shugaban karamar hukumar tare da wasu mazauna yankin hudu zuwa cikin daji.

Yunusa ya ce harin ya fara tsakanin karfe 10:40 zuwa 10:50 na dare, kuma ya dauki sama da sa'o'i biyu ana gudanar da shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga kusan 200 sanye da kayan sojoji sun yi ta'asa a jihar Sokoto

Ya yi zargin cewa jami'an tsaro sun yi jinkirin kai dauki, yana cewa da sun iso da wuri da ba a yi garkuwa da su ba, cewar Punch.

Wani dan uwa, Anas Ibrahim, ya ce mazauna garin sun lura da motsin wasu mutane masu ban mamaki tun kafin harin kuma sun sanar da jami'an tsaro.

Ya kara da cewa abin takaici ne yadda 'yan bindiga suka gudanar da harin na tsawon lokaci a tsakiyar Bungudu ba tare da wani ya dakile su ba, kafin su tsere da shugaban karamar hukumar.

Yan bindiga sun sace babban alkali a Kebbi

Mun ba ku labarin cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da alkalin babbar kotun Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, a gidansa da ke karamar hukumar Bunza.

Iyalansa sun ce maharan sun bi shi tun daga Sokoto, sannan suka harbe-harbe kafin su tafi da shi kan babura.

Lamarin ya kara tayar da hankali kan matsalar tsaro a Kebbi, duk da cewa Bunza ba ta cikin wuraren da hare-haren 'yan bindiga suka fi kamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.