Mutum 20 sun mutu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto

Mutum 20 sun mutu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto

- Kimanin mutum 20 sun rasu sakamakon wani mummunan hatsari a garin Tureta da ke Jihar Sokoto

- Har wa yau kimanin mutane 14 sun jikkata inda aka garzaya da su asbitin UDUTH inda suke karbar magani

- Wasu mazauna Tureta sun ce gudu fiye da kima da direbobin motoccin haya ke yi a titin ne ya janyo hatsarin

A kalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin mota da ya faru a karamar hukumar Tureta da ke Jihar Sokoto kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A cewar shaidun ido, lamarin ya faru ne a kauyen Bimasa misalin karfe 6 na yamma a ranar Alhamis a yayin da mota kirar Gulf ta yi karo da wata Toyota Hiace dauke da fasinjoji.

Mutum 20 sun mutu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto
Mutum 20 sun mutu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto. Hoto: @LeadershipNGA
Source: Twitter

DUBA WANNAN: A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

"Abin babu dadin kallo. Mun kirga a kalla fasinjoji 20 da suka mutu a nan take yayinda wasu da dama sun samu munanan raunuka," a cewar wani mazaunin kauyen da ya ziyarci inda abin ya faru.

Kakakin 'yan sandan Jihar Sokoto, Sadiq Abubakar a jiya ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum 19, inda ya kara da cewa wasu mutum 14 da suka jikkata sakamakon hatsarin suna samun kulawa a asibitin koyarwa ta Jami'ar Danfodio, UDUTH, da ke Sokoto.

KU KARANTA: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Wani shaidan ganin ido, Malam Nura, ya ce idan ba don gudun da direban Gulf din ya ke yi ba da hatsarin bai faru ba.

"Kaga akwai rami sosai a titin amma duk da hakan direbobin Gulf da Sharon na haya sukan rika zura gudu tamkar za su tafi lahira," in ji shi.

Ya cigaba da cewa hatsari musamman na motoccin Gulf da Sharon ya zama ruwan dare a titin don haka ya yi kira ga FREMA ta cike ramukan da ke titin. Ya kuma yi kira ga FRSC ta rika yi wa direbobi gwajin muggan kwayoyi

A wani labarin daban, Kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel