‘Jirgi Marar Matuki Zan Nada’: Sowore kan Wanda Zai ba Ministan Tsaro Idan Ya Ci Mulki
- Dan takarar shugabancin Najeriya na AAC, Omoyele Sowore, ya yi magana game da yadda rashn tsaro ya tabarbare a Najeriya
- Sowore ya bayyana cewa zai yi amfani da jirage marasa matuka a matsayin Ministan Tsaro idan ya lashe a 2027
- Ya ce zai kafa cibiyar kula da tsaro da za ta bibiyi masu ta’addanci tare da dakile su cikin gaggawa ta amfani da fasaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke kara kamari a Najerya.
Sowore ya yi alƙawarin amfani da jirage marasa matuka a matsayin Ministan Tsaro idan ya zama shugaban Najeriya a 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikn wata hira da dan gwagwarmayar ya yi da gidan talabijin na Arise wanda wakiln Legt Hausa ya bibiya a jiya Alhamis 28 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya
2027: Alkawuran da Sowore ya daukarwa yan Najeriya
Sowore ya ce zai kafa wata cibiyar kula da tsaro wadda za ta rika bin diddigin ‘yan ta’adda tare da dakile su cikin gaggawa ta hanyar amfani da fasahar zamani.
'Dan gwagwarmayar ya ce zai magance matsalar rashin tsaro kai tsaye ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro da fasaha.
Ya ce:
“A gajeren lokaci, dole mu tunkari rashin tsaro kai tsaye ta hanyar fatattakar ‘yan bindiga da haɗin gwiwar aiki da kayan aiki na zamani da bayanan sirri.”
Ya ƙara da cewa dole ne a samu shugabannin tsaro masu gaskiya da rikon amana, ba siyasa ko raba hankali ba, tare da rundunar soja da ‘yan sanda masu dabarun aiki na gaskiya.

Source: Facebook
Yadda Sowore zai magance matsalar tsaro a Najeriya
Sowore ya ce za a kafa cibiyar kula da tsaro ta tsakiya domin bibiyar barazana cikin lokaci da kuma dakile ƙungiyoyin masu laifi don tsaron ƙasa.
Ya ce:
“Idan na zama shugaban ƙasa gobe, Ministan Tsarona zai zama jirage marasa matuka, saboda haka na yi imani da fasaha sosai.”
Ya ƙara da cewa wadannan jirage marasa matuka za su rika yawo ko’ na, yayin da za a kafa cibiyar da mutane za su rika bin diddigin ‘yan ta’adda domin kawo karshen hare-haren da ake kai wa al'umma baki daya.
Amma ya jaddada cewa dole ne a samar da al’umma inda mutane za su samu aiki, su je makaranta, ba tare da shiga wasu ayyukan laifuffuka wanda ya ce hakan ne kadai za taimaka masa domin cimma burinsa.
Dadiyata: Sowore ya zargi Ganduje, El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya bukaci a gayyaci wasu manya a Najeriya domin amsa tambayoyi kan batan Abubakar Idris watau Dadiyata.
Sowore ya nuna rashin amincewa da binciken rundunar ‘yan sanda, yana mai neman a kafa kwamitin bincike na shari’a mai zaman kansa.
Dadiyata ya bace tun kusan shekaru bakwai bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace shi daga gidansa da ke Kaduna.
Asali: Legit.ng
