‘Yadda Tinubu Ya Sadaukar da Komai domin Ceto ’Yan Najeriya daga Halin Kunci’

‘Yadda Tinubu Ya Sadaukar da Komai domin Ceto ’Yan Najeriya daga Halin Kunci’

  • Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya bayyana kokarin Bola Tinubu ya yi wurin ceto Najeriya
  • Hadimin shugaban kasar ya ce Bola Tinubu ya “sadaukar da komai” domin ceton Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki da tabewa
  • Ya ce sauye-sauyen Tinubu kamar cire tallafin mai da daidaita darajar naira sun taimaka wajen ƙara kuɗin jihohi da ayyukan ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu.

Onanuga ya bayyana cewa shugaban ya gwammace ya sha wahala domin ceton Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki.

An bayyana yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga durkushewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a hagu, da kuma wani lokaci yana shirin hawa jirgin sama. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Onanuga, a cikin rubutunsa da ya wallafa a X inda ya ce ‘yan adawa na yaɗa ƙarya duk da nasarorin gwamnati cikin shekaru uku.

Kara karanta wannan

Tinubu: "Yadda muka ceto Najeriya daga rugujewa a shekaru 3 na mulkina"

Matsaloln da Bola Tinubu ya samu a Najeriya

Ya ce Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu 2023 a lokacin da tattalin arziki ke cikin matsala mai tsanani, ciki har da ƙarancin mai, hauhawar bashi da tsarin musayar kuɗi marar daidaito.

A cewarsa, matakan gaggawa na cire tallafin man fetur da daidaita darajar Naira sun kasance masu zafi amma sun taimaka wajen hana rugujewar tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa wadannan sauye-sauye sun ƙara kuɗaɗen da jihohi ke samu, wanda ya ba su damar biyan albashi da aiwatar da ayyukan ci gaba.

Hadimin Tinubu ya kare matakan shugaban kasa kan tattalin arziki
Hadimin Bola Tinubu a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Mulkin Tinubu: Yadda jihohi suka samu ci gaba

Onanuga ya ce jihohi da dama yanzu na ganin ci gaba a ayyukan more rayuwa, sakamakon gyaran tsarin kuɗi da gwamnatin tarayya ta yi.

Ya kuma ce lokacin da ƙananan hukumomi suka fara karɓar kuɗaɗensu kai tsaye, mulki zai ƙara gangarowa zuwa matakin ƙasa.

Ya ce gwamnonin jihohi da dama sun amince cewa manufofin Tinubu sun taimaka musu wajen aiwatar da manyan ayyuka na ci gaba.

Kara karanta wannan

"A tattara a koma jihar Legas": Atiku Ya Fara Aika Zafafan Sakonni ga Tinubu

Ya kuma bayyana cewa kasuwar hannun jari ta ƙaru sosai daga maki 53,000 zuwa 250,000, tare da ƙaruwa a darajar kasuwa daga N30tn zuwa N160tn.

Onanuga ya ƙara da cewa an yi gyare-gyare a harkar jiragen ƙasa, mai da iskar gas, da shirye-shiryen lamunin ɗalibai da sauran shirye-shiryen taimakon jama’a.

Ya ce duk da ƙalubalen tsaro, gwamnati na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki da haɗin gwiwar ƙasashen waje.

A cewarsa, tarihi zai tuna gwamnatin Tinubu da manyan sauye-sauye da ayyukan da suka sauya fuskar tattalin arzikin Najeriya.

Atiku ya sake caccakar salon mulkin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce Bola Tinubu ya gaza matuka wajen magance matsalar tsaro.

Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki domin tabbatar da kubutar da daliban makaranta da aka sace a jihohin Oyo da Borno.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga Tinubu ya sauka, ya nuna damuwa kan tabarbarewar matsalar tsaro a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.