An Fasa Yanka Saniyar da Ke ‘Kama’ da Trump a Layya, Gwamnati Ta Shiga Lamarin

An Fasa Yanka Saniyar da Ke ‘Kama’ da Trump a Layya, Gwamnati Ta Shiga Lamarin

  • Gwamnatin kasar Bangladesh ta dakatar da yanka wata farar saniya mai suna “Donald Trump” bayan yada ta a kafofin sadarwa
  • Ministan harkokin cikin gida ya bayar da umarnin a ceci dabbar tare da mayar wa mai saye kudinsa saboda matsalar tsaro
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutane daga wurare daban-daban sun rika zuwa ganin saniyar saboda farin gashinta da yanayin nutsuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dhaka, Bangladesh - Wata farar saniya mai suna “Donald Trump” a Bangladesh ta tsira daga shirin yanka ta a layya da aka gudanar a jiya Laraba 27 ga watan Mayun 2026.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an fasa yanka ta ne bayan gwamnatin kasar ta shiga lamarin a karshe domin matsalat tsaro.

An fasa yanka saniyar da ke kama da Trump a Bangladesh
Shugaba Donald Trump da wata saniya mai kama da shugaban Amurka. Hoto: Abdul Goni/Anadolu.
Source: Getty Images

An bayyana cewa saniyar mai kimanin nauyin kilo 700 an riga an sayar da ita domin hadayar salla kafin gwamnati ta dakatar da shirin yankata, cewar Sky News.

Kara karanta wannan

Babbar salla: Tinubu ya saukaka wa yan kasa, ya rage kudin sufurin jiragen kasa

Dalilin fasa yanka saniyar a layya

Wani jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ya ce gwamnati ta dauki matakin ne saboda matsalar tsaro da kuma yawaitar sha’awar jama’a game da dabbar.

Ministan harkokin cikin gida a kasar Bangladesh, Salahuddin Ahmed, ya bayar da umarnin a ceci saniyar tare da mayar wa wanda ya saya kudinsa bayan dakatar da hadayar.

Daga bisani an kai dabbar zuwa gidan namun daji na kasa da ke Dhaka bayan bidiyonta sun bazu sosai a kafafen sada zumunta daban-daban.

Mutane da dama sun rika tururuwa zuwa wurin dabbar domin ganin farin gashinta da halinta na nutsuwa wanda ya sa ake kwatanta ta da Donald Trump.

Mai dabbar, Ziauddin Mridha, ya bayyana cewa kaninsa ne ya ba ta sunan Donald Trump saboda kamannin farin gashinta da shugaban Amurka.

Ya kara da cewa saniyar tana da matukar nutsuwa kuma tana bukatar kulawa ta musamman da suka hada da yawan ciyarwa da yi mata wanka akai-akai.

Kara karanta wannan

Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki

Rahoton ya bayyana cewa irin wadannan fararen shanu ba safai ake samun su a Bangladesh ba, lamarin da ya sa dabbar ta yi fice sosai lokacin salla, cewar Reuters.

An dauke saniya mai 'kama' da Trump zuwa gidan 'zoo' a Bangladesh
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Matakin yan sanda kan saniya a Bangladesh

Ruhul Quddus, jami’in kula da ofishin ‘yan sanda na Keraniganj, ya ce hukumomi sun dauke dabbar daga yankin Rasulpur da misalin karfe 5 na yamma.

Ya ce:

“Da taimakon ma’aikatar harkokin cikin gida, an dauko saniyar daga yankin Rasulpur da misalin karfe 5 na yamma.”

Majiyoyi sun rawaito Quddus na cewa ofishin jakadancin Amurka bai so a yanka saniyar ba domin layya.

Har yanzu hukumomi ba su sanar da wani mataki ko hukunci da za a dauka kan dabbar nan gaba ba.

Trump ya magantu bayan hari a White House

Mun ba ku labarin cewa shugaba Trump ya ce maharin da ya kai hari White House yana da yiwuwar sha’awar fadar tare da yabawa jami’an DSS kan kokarinsu.

Nasire Best mai shekara 21 ya bude wuta a kofar tsaro Washington DC jami’an tsaro sun mayar da martani suka kashe shi nan take.

Bincike ya nuna maharin ya taba karya umarnin kotu ya hana shi kusantar White House sannan ya sha fama da matsalolin bin doka a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.