‘Na Cika Kusan Duka Alkawuran da Nayi ga Yan Kano’: Abba Kabir Ya Bugi Kirji
- Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru uku da ya yi yana mulki a jihar
- Abba Kabir ya ce ya cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawuran da ta yi wa jama’a cikin shekaru uku da ya yi a mulki
- Ya bayyana hakan ne yayin taron Sallah da ya karɓi Sarkin Rano, yana mai cewa ana ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba a sassa daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru uku da ya yi a mulki.
Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawuran da ta ɗauka wa al’ummar jihar cikin shekaru uku na mulki.

Source: Facebook
Ya yi wannan bayani ne a fadar gwamnati yayin da ya karɓi Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, a ziyarar Sallah da ya kai masa, cewar Punch.
Ci gaban da aka samu a Kano
A cewarsa, an samu ci gaba a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, samar da ruwa, ababen more rayuwa da ƙarfafa matasa domin inganta rayuwar jama’a.
Gwamnan ya ce burin gwamnatinsa shi ne inganta rayuwar al’umma da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a duk fadin jihar Kano.
Ya ƙara da cewa za a kammala sauran ayyukan da suka rage kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa, tare da ci gaba da aiwatar da sabbin ayyuka.
A cewarsa:
“Ina farin cikin bayyana cewa gwamnatarmu ta cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawuran da muka yi wa al’ummar Jihar Kano cikin shekaru uku da muka hau mulki.
“Gwamnatarmu ta zo da tsayayyen hangen nesa na inganta rayuwar jama’armu, kuma Alhamdulillah, mun samu gagarumin ci gaba a muhimman fannoni da ke shafar jin daɗin al’umma kai tsaye.”

Source: Facebook
Abba Kabir ya yi wa yan Rano alkawari
Abba ya kuma tabbatar wa al’ummar masarautar Rano cewa manyan ayyuka kamar titin Karfi–Rano da gyaran fadar sarki za su samu kulawa ta musamman.
A nasa jawabin, Sarkin Rano ya yaba da ayyukan ci gaba da aka gudanar a yankin cikin shekaru uku na gwamnatin Abba Yusuf.
Ya ambaci gina tituna a Rano, Kibiya da Bunkure, da kuma cigaban aikin ruwa na Kaluwaiwai a matsayin manyan nasarori.
Sarkin ya kuma yabawa kokarin gwamnati wajen inganta asibiti da makarantu, yana mai cewa hakan zai amfani al’umma na tsawon lokaci.
Ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan masarautar Rano ga gwamnatin Kano wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, cewar Daily Post.
Aminu Gwarzo ya caccaki mulkin Abba Kabir
A wani labarin, mun ba ku labarin cewa dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kakkausar suka kan yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a jihar.
Ya ce hare-haren da ake kai wa al’umma a wasu ƙananan hukumomi sun nuna cewa rayuka da dukiyoyin jama’a ba sa samun kariya yadda ya kamata.
Kwamred Aminu Gwarzo ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankunan Kano.
Asali: Legit.ng


