An Dauke Ministan Buhari daga Ofishin EFCC, An Mayar da Shi Gidan Yarin Kuje

An Dauke Ministan Buhari daga Ofishin EFCC, An Mayar da Shi Gidan Yarin Kuje

  • EFCC ta kai tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, gidan yari na Kuje bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 a kurkuku
  • Kotun tarayya ta bayyana cewa Mamman ya tsere zuwa Kaduna bayan an yanke masa hukunci duk da yana Abuja a lokacin shari’ar
  • Hukumar EFCC ta kuma nemi kotu ta ƙwace wasu kadarori biyar da ake zargin suna da alaƙa da tsohon ministan a Abuja da Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar EFCC ta kai tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja bayan kotu ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa.

Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya bayar da umarnin kai shi gidan yarin ranar Talata.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

EFCC ta mika tsohon ministan wutar lantarki zuwa gidan yari.
Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman a ofishin EFCC sanye da ankwa. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Yadda aka yanke wa tsohon minista hukunci

A ranar 7 ga watan Mayu ne kotu ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume 12 da EFCC ta shigar a kansa, kamar yadda hukumar ta sanar a shafinta na Facebook.

Daga bisani aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari ba tare da yana kotu ba.

Kotun ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai-bakwai a kan tuhume-tuhume 10, yayin da aka yanke masa shekaru uku da biyu a wasu tuhume-tuhume daban.

Mai shari’ar ya bayyana cewa hukuncin zai gudana ne ɗaya bayan ɗaya ba tare da zaɓin tara ba, sai dai a tuhuma ta huɗu da aka ba shi damar biyan tara ta Naira miliyan 10.

Tsohon minista ya tsere zuwa Kaduna

A yayin zaman kotun ranar Talata, wani ɗan uwansa mai suna Shamsudeen Mohammed ya shaida wa kotu cewa Mamman yana Abuja lokacin da aka yanke masa hukunci kafin daga bisani ya tsere zuwa Kaduna cikin tasi bayan kwana biyu.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Kotu ta kawo karshen shari'ar Jonathan kan takarar shugaban kasa a 2027

Ya ce:

“Yana fama da rashin lafiya kuma ni ne mai taimaka masa wajen shan maganin gargajiya. An kawo shi Kaduna daga Abuja cikin tasi.”

Sai dai ya ce bai san mai gidan da Mamman ya buya a Rigasa da ke Kaduna ba.

Alkali ya yi masa bayani

Da yake jawabi, mai shari’a ya ce hukuncin gidan yarin Mamman ya fara aiki nan take daga ranar Talata.

Ya ce:

“Kana Abuja lokacin da aka yanke hukuncin. Kai kaɗai ka tafi Kaduna cikin tasi. Na gama aikina, amma dole na sanar da kai cewa yau ne fara aiwatar da hukuncin.”

EFCC ta nemi ƙwace kadarori

A yayin shari’ar, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya nemi kotu ta bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori biyar da ake alaƙanta wa da Saleh Mamman.

EFCC ta ce ta kamo Saleh Mamman a wani gida da ke Rigasa, Kaduna inda yake buya.
Saleh Mamman rike da allon EFCC bayan an kama shi a Kaduna. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Kadarorin sun haɗa da Walijam Apartments da ke Wuse 2 Abuja, Bloom Luxury Suites da ke Kaduna, wasu manyan gidaje biyu a Misratah Street da kuma A.U.A Plaza da ke Wuse 2 Abuja.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Yadda matafiya za su kauce wa cunkoso a hanyar Abuja zuwa Kaduna

EFCC ta ce lauyan Mamman bai halarci kotu ba duk da an sanar da shi batun neman ƙwace kadarorin.

Da kotu ta tambayi Mamman dalilin rashin zuwan lauyansa, ya ce tun bayan kama shi a ranar 19 ga watan Mayu bai sake samun damar tuntuɓarsa ba.

Daga bisani mai shari’a ya ɗage sauraron buƙatar ƙwace kadarorin zuwa ranar 8 ga watan Yunin 2026 domin tabbatar da adalci.

Karanta sanarwar EFCC a nan kasa:

EFCC ta kamo Saleh Mamman a Kaduna

Tun da fari, mun ruwaito cewa, EFCC ta sanar da cafke tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, bayan hukuncin kotu kan laifin karkatar da kudade.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an kama Saleh Mamman ne da misalin karfe 3:30 na safiyar Talata a yankin Rigasa da ke Kaduna.

EFCC ta bayyana cewa ana boye tsohon ministan a cikin wani gida, yayin da aka kama wasu mutum biyu da suke ba shi kariya a gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com