Jami'an EFCC Sun Kutsa cikin Wani Gida, Sun Cafko Ministan Buhari da Ake Nema
- Hukumar EFCC ta sanar da cafke tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, bayan hukuncin kotu kan laifin karkatar da kudade
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an kama Saleh Mamman ne da misalin karfe 3:30 na safiyar Talata a yankin Rigasa da ke Kaduna
- EFCC ta bayyana cewa ana boye tsohon ministan a cikin wani gida, yayin da aka kama wasu mutum biyu da suke ba shi kariya a gidan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta sanar da cewa jami'anta sun samu nasarar cafke tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman.
EFCC ta cafke Saleh Mamman, bayan kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukunci kan laifin karkatar da kudade yayin da yake rike da mukamin minista.

Source: Facebook
Saleh Mamman: EFCC ta kama ministan Buhari
A cikin jawabin da shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya yi wa 'yan jarida, kuma aka wallafa a shafin hukumar na X, an tabbatar da cafke tsohon ministan a ranar Talata.
A cewar Ola Olukoyede, an kama tsohon ministan wutar lantarkin, Saleh Mamman ne da misalin karfe 3:30 na safiya a jihar Kaduna.
“Ina farin cikin sanar da ‘yan Najeriya cewa da misalin karfe 3:30 na safiyar yau mun kama Mista Saleh Mamman a wani wuri da ke Rigasa a jihar Kaduna.”
- Ola Olukoyede.
“Wannan gwaji ne ga yaki da rashawa”
Shugaban EFCC ya bayyana cewa kamun tsohon ministan wani muhimmin mataki ne da ke nuna kudirin gwamnatin tarayya na yaki da cin hanci da rashawa.
Ya ce:
“Wannan gwaji ne na kudirin gwamnatin tarayyar Najeriya wajen yaki da rashawa da kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa duk wanda ya wawuri dukiyar kasa ba zai tsira daga hukunci ba.”
Olukoyede ya kara da cewa idanun EFCC za su ci gaba da bibiyar duk wanda ake nema ruwa a jallo kan almundahanar kudade ko da inda yake boye.
EFCC ta ce ana boye tsohon ministan
Shugaban hukumar ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa ana boye Saleh Mamman tare da ba shi kariya.
Ya ce:
“Mun gano cewa ana kare shi tare da boye shi duk wannan lokaci.”
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun kama wasu mutum biyu tare da tsohon ministan yayin samamen da suka kai.

Source: Twitter
An ce mutanen biyu na tare da shi ne lokacin da aka kama shi, kuma jami’an tsaro na gudanar da bincike kan gidan da aka cafke shi a ciki.
“Masu gidan ma na karkashin bincike saboda laifi ne mutum ya boye ko ya ba da kariya ga wanda aka yankewa hukunci.”
- Ola Olukoyede.
Kalli sanarwar shugaban EFCC a kasa:
Kotu ta daure Saleh Mamman
Tun da fari, mun ruwaito cewa, babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan wuta, Saleh Mamman hukunci kan zargin badakalar N33.8bn.

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke wa Halima Umar hukunci bayan kama ta da makamai masu hadari a Filato
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 bisa zargin satar kudaden gwamnati da suka kai kusan N33.8bn, a shari'ar da EFCC ta shigar.
Alkalin kotu ya ce an tabbatar da laifuffukan damfara da safarar kudi da EFCC ta gabatar, inda aka ba shi hukunci mai gudana ba tare da zabin tara ba.
Asali: Legit.ng

