‘Ni Na Hada Kwankwaso da Tinubu domin a ba Shi Minista’: Dan Majalisar Kano
- 'Dan majalisar tarayya daga jihar Kano ya ce son kai da burin mukami ne suka hana Rabiu Kwankwaso shiga jam'iyyar APC ba komai ba
- Babban 'dan siyasar ya bayyana cewa shi ne ya hada ganawar Kwankwaso da Tinubu, inda aka yi masa alkawarin mukamin minista kafin ya ki shiga APC
- 'Dan siyasar ya ce Kwankwaso ya koma NDC ne bayan ya fahimci ba zai samu burinsa na samun shugaban kasa ko mataimaki a ADC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini ya yi magana kan halayen Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a siyasa.
Ali Madaki ya ce sun san dalilin da ya sa Rabiu Kwankwaso bai shiga APC ba sabanin abin da wasu mutane suke tunani kansa.

Kara karanta wannan
"Ana rasa abinci a gidana": Ministan Buhari, Amaechi ya magantu kan mulki a Najeriya

Source: Facebook
Dan majalisar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Dokin Karfe ya yi hira da shi wanda aka wallafa a Facebook.
Yadda Madakin-Gini ya haɗa Tinubu da Kwankwaso
A cikin bidiyon, Madaki mai wakiltar yankin Dala ya ce son kai da burin zama shugaban kasa ko mataimaki shi ya hana Kwankwaso shiga APC a Najeriya.
Ya ce shi da kansa ya hada ganawar Kwankwaso da Tinubu domin a ba shi minista amma ba haka ba ne burin tsohon gwamnan kuma ba al'umma ba ne a gabansa.
Ya ce:
"Duk wani haduwa da shugaban kasa da ki ka ga Rabiu Kwankwaso ya yi, ni da kike gani, ni na hada zaman da aka yi shi.
"Ni na tsara yadda aka yi Kwankwaso ya fara zuwa fadar shugaban kasa aka yi magana na alkawarin za a ba shi minista.
"Saboda haka babu wani dalili na Kwankwaso na kin shiga APC sai kawai don bukatarsa ta karan kansa ba ta jama'a, Arewa ko addini ba."

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Source: Facebook
Madaki ya bayyana burin Kwankwaso a siyasa
Dan majalisar ya ce mutane da yawa sun dauka butukcewa Kwankwaso suka yi amma ba su san halayensa ba ne shiyasa.
"Bukatar Kwankwaso na zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa shi ne dalilinsa na kin shiga APC.
"Da ya shiga ADC, sai kuma ya ga fa wannan bukata ta shi ba za ta biya a ADC ba, sai ya zuga Peter Obi ya dauke shi suka koma NDC domin takarar mataimakin shugaban kasa.
"Shiyasa na ce miki na ji dadin wannan abin, muna fadawa mutane ga yadda yake da dalilin rabuwar mu da shi da yawa mutane ba su yarda kuma suna ganin ba gaskiya ba ne.
"Ko kuma wasu su ce butulci muka yi, to ga shi kowa ya gane shi idan shi dai ba lamba daya ba ne, to ba a yi ba, shiyasa ya ki shiga APC."
- Aliyu Sani Madakin Gini

Kara karanta wannan
Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu
Hadimin Abba ya zargi Kwankwaso kan zaben 2027
Mun ba ku labarin cewa Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature D/Tofa, ya yi tsokaci kan wasu abubuwan da suka faru a siyasar Kano.
Sanusi Bature ya bayyana cewa da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka tuntubi Shugaba Bola Tinubu don komawa jam'iyyar APC.
Hadimin na gwamnan Kano ya kuma zargi madugun na Kwankwasiyya da yi wa Shugaba Tinubu aiki don zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng