2027: APC Ta Raba Gardama, Ta Tsaida 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Filato da Adamawa
- Jam'iyyar APC ta tsayar da 'yan takarar gwamna a jihohin Adamawa da Filato bayan kammala zabukan fitar da gwani
- Gwamna Caleb Mutfwang ya doke abokin takararsa, John Peter, inda ya samu tikitin APC na neman tazarce a zaben gwamnoni na 2027
- A jihar Adamawa kuwa, APC ta ayyana Ahmed Tijjani Galadima a matsayin wanda ya lashe zaben tsaida dan takarar gwamna da aka gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC, Fidelis Mnyim, ya ayyana gwamna Caleb Mutfwang, a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Filato a zaben 2027.
Yayin bayyana sakamakon bayan kammala zaɓen a ofishin jam’iyyar da ke Jos, Mnyim ya ce Barrista Caleb Manasseh Mutfwang ya samu jimillar ƙuri’u 233,335.

Source: Facebook
Gwamna Caleb Mutfwang ya samu tikitin APC
A rahoton da Channels tv ta wallaha, gwamnan ya kayar da abokin takararsa, John Peter, wanda ya samu ƙuri’u 3,070.
Fidelis Mnyim ya ce:
“Barrista Caleb Manasseh Mutfwang, bayan ya cika dukkan sharuɗɗan kundin tsarin mulkin APC da ƙa’idojinta kuma ya samu mafi yawan ƙuri’u, na ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a Jihar Filato.”
Bayan ayyana sakamakon, magoya bayan gwamnan sun barke da murna a cibiyar tattara sakamako yayin da jami’an jam’iyyar APC suka kammala sanya hannu kan takardun sakamako.
Mnyim ya yaba wa mambobin APC bisa yadda suka gudanar da kansu cikin lumana a lokacin zaɓen a fadin mazabun jihar Filato.
APC ta tsaida ɗan takarar gwamnan Adamawa
Hakazalika, kwamitin zaɓen APC a jihar Adamawa ya ayyana Ahmad Tijjani Galadima a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna gabanin babban zaɓen 2027, cewar rahoton Leadership.
Yayin sanar da sakamakon a Yola, babban birnin jihar, shugaban kwamitin, Innocent Bariko, ya ce an samu wannan sakamako ne bayan tattara ƙuri’u daga ƙananan hukumomin Adamawa.
Da yake jawabin godiya, Tijjani Galadima ya bayyana cewa nasarar da ya samu ci gaba ce ga jam’iyyar APC, tare da kira ga sauran masu neman takara da su haɗa kai domin ganin APC ta samu nasara a babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Sai dai gudanar da zaɓen bai rasa koke-koke ba, domin wasu daga cikin magoya bayan ‘yan takarar sun nuna rashin gamsuwa kan abin da suka kira rashin gaskiya wajen gudanar da zaɓen.
Bayan bayyana sakamakon, yanzu ana sa ran waɗanda ba su gamsu ba za su shigar da ƙorafe-ƙorafensu, yayin da kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe na APC zai tattara duka ya duba.
APC ta raba gardama a jihar Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi, ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a jihar.
Danladi ya kayar da sauran masu neman takara 14, ciki har da wani sanata mai ci, a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 16 na jihar Kwara, inda ya samu ƙuri’u 94,990.
Shugaban kwamitin fitar da gwanin APC kuma tsohon ƙaramin ministan tsaro, Musiliu Obanikoro, ne ya sanar da sakamakon a Banquet Hall da ke Ilorin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

