Ragunan Layya Sun Yi Tashin Gwauron Zabi Ana Shirin Babbar Sallah a Jihar Kaduna

Ragunan Layya Sun Yi Tashin Gwauron Zabi Ana Shirin Babbar Sallah a Jihar Kaduna

  • Farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi a wsu kasuwannin jihar Kaduna kafin yayin da musulmi ke shirye-shiryen sallar layya
  • Bincike ya nuna cewa farashin dan matsakaicin rago da bai kai ga girma sosai ba ya tashi daga N150,000 zuwa N250,000
  • Masu saye da dillalai sun danganta tashin farashin da matsin tattalin arziki da matsalar tsaron da ake fama da su a sassan kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Yayin da al’ummar Musulmi ke shirin bukuwan sallar layya (Eid-el-Kabir), farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi a jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya sa mutane da dama sun dakatar da sayen dabbar da za su yi layya da ita duk da wadatar dabbobin a kasuwanni.

Ragunan layya.
Ragunan layya a wata kasuwar dabbobi a Najeriya Hoto: Bello Ado Muhammed
Source: Facebook

Binciken da Vanguard ta gudanar a wasu manyan kasuwannin dabbobi da ke cikin birnin Kaduna ya nuna cewa kasuwannin sun cika da raguna, amma babu masu saye.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Malamin addini da matarsa sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

A kasuwannin Zango, Rigasa da Bashama Road, ana sayar da kananan raguna tsakanin N150,000 zuwa N250,000, yayin da matsakaita da manyan raguna ke kaiwa daga N300,000 har zuwa Naira miliyan 1, gwargwadon iri da girmansu.

Mazauna Kaduna sun koka da tsadar raguna

Wasu mazauna jihar Kaduna sun bayyana cewa farashin ya yi tsada sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Wani magidanci, Abdulrahman Usman, wanda aka gani yana cinikin rago a kasuwar Zango, ya nuna damuwa kan yadda farashin dabbobin ya yi tashin gwauron zabi.

Sai dai ya ce yana fatan farashin zai sauka yayin da ranar Sallah ke kara matsowa.

Wani dillalin dabbobi a kasuwar Rigasa, Alhaji Suleiman Adamu, ya danganta tashin farashin da tsadar sufuri, abincin dabbobi da kuma matsalar tsaro da ke shafar hanyoyin safara.

A cewarsa, karin kudin kula da dabbobin kafin a sayar da su ma ya taimaka wajen tashin farashin, kamar yadda Punch ta kawo.

Wasu raguna sun kai N700,000

Shi ma wani dillali, Bilyaminu Musa, ya ce yana kawo raguna daga jihar Neja domin abokan huldarsa na musamman.

“Na shafe kusan shekara 10 ina wannan kasuwanci. Ina kawo raguna ga abokan ciniki na na musamman da suka san darajar irin wadannan raguna,” in ji Musa.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun kara farashin buhun siminti a Najeriya, yanzu ya haura N12,500

Ya bayyana cewa daga cikin raguna 40 da ya kawo, an riga an sayar da guda 14.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Da aka tambaye shi farashin mafi kankanta da mafi girman rago, ya ce mafi kankanta shi ne ragon N350,000 ne yayin da mafi girma ya kai N700,000.

Wasu mazauna Kaduna sun nuna damuwa kan tsadar raguna, inda suka shaida wa Legit Hausa cewa layya na neman ta gagari talata

Aliyu Zaharadeen ya ce shi ya riga ya hakura da batun layya, domin albashin da yake samu da sana'arsa ba su kai karfin da zai ware N300,000 zuwa N500,000 ya sayi rago ba.

"Ina da iyali da iyaye, maganar gaskiya tsadar ta yi yawa, tun da ba wajibi bane mun hakura da batun layya a wannan Sallah, Allah Ya karbi ibadunmu," in ji shi

An ba da hutun babbar sallah a Turkiyya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Recep Erdoğan ya ba da sanarwar ƙara hutun Sallar Layya na shekarar 2026 zuwa kwanaki tara ga ma'aikatan gwamnati a Turkiyya

Kara karanta wannan

Yahudawa sun bankawa masallaci, motoci wuta yayin ibada a Isra'ila

Bukukuwan sallar za su fada tsakanin 27 zuwa 30 ga watan Mayu 2026, amma dai yanzu an haɗe su da kwanakin aiki na Litinin da Talata don samun hutu mai tsawo.

Sallar layya, wadda Turkawa ke kira da Kurban Bayram, tana ɗaya daga cikin manyan bukukuwan Musulunci da ake gudanarwa don tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262