Lokaci Ya Yi: Alkalin Babbar Kotun Tarayya ta Kano, Mohammed Yunusa Ya Yi Mutuwar Fuju'a
- Alƙalin babbar kotun tarayya reshen Jihar Kano, Mai Shari'a Mohammed Nasir Yunusa ya rasu bayan ya fadi a falon gidansa
- Daraktar yaɗa labarai ta Kotun Tarayya ta Najeriya, Catherine Oby Christopher, ta ce Mai Shari'a Yunusa ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano
- Marigayi alkalin ya jagoranci manyan shari'o'i a rayuwarsa ciki har da batun halascin shiga zaben 'yan takarar jam'iyyar LP a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - 'Daya daga cikin sanannun alƙalin babbar kotun tarayya reshen Jihar Kano, Mohammed Nasir Yunusa, ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a falon gidansa.
Rahotanni sun ce alƙalin ya faɗi ne a ɗakin hutawarsa watau falo, inda aka garzaya da shi asibiti, amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan
"Ku zabe ni": Amaechi ya bayyana shirinsa ga 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa

Source: Getty Images
An yi jana'izar Mai Shari'a Yunusa
Majiyoyi daga cikin Kotun Tarayya da ke Abuja sun shaida wa Daily Trust a ranar Asabar cewa an binlrne marigayin ranar Juma’a bisa tanadin addinin Musulunci.
Wata majiya ta ce:
“Eh, alƙalin ya rasu ne da yammacin Alhamis kuma an riga an birne shi. Mutum ne mai ƙwazo sosai a rayuwarsa. Ka san ya jagoranci shari’o’i masu muhimmanci kuma yana gudanar da adalci yadda ya dace.”
Kotun tarayya ta tabbatar da lamarin
Daraktar yaɗa labarai ta Kotun Tarayya ta Najeriya, Catherine Oby Christopher, ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce Mai Shari'a Yunusa ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano.
An ruwaito cewa ɗaya daga cikin manyan shari’o’in da marigayin ya jagoranta shi ne bayan zaɓen 2023, lokacin da Kotun Tarayya da ke Kano ta musanta cewa ta soke takarar zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia a lokacin, Alex Otti.
A lokacin, kotun ta soke zaɓen ‘yan takarar jam’iyyar LP a Kano da suka fafata a babban zaɓen 2023.
Hukuncin da marigayin ya yanke
Sai dai mai shari'a Mohammed Yunusa ya bayyana cewa ‘yan takarar da suka shiga zaɓe a jihar Abia ba su cikin waɗanda aka shigar da ƙara a kansu a gabansa.
Ya ce:
“Wannan kotu ba ta da hurumin bayar da umarnin ba da takardar shaidar cin zaɓe. Suna da damar neman mafita a sashen kotun da ya dace.”

Source: Facebook
Lamarin ya samo asali ne bayan wani mai ƙara, Ibrahim Haruna-Ibrahim, ya nemi kotun ta soke takardun shaidar cin zaɓe da aka bai wa dukab‘yan takarar LP da suka yi nasara a Kano da sauran jihohi 35 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wadanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da jam’iyyar LP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yayan tsohon minista, Sylva ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa Cif Johnbull Anagha Sylva, babban yayan tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon ministan fetur,, Timipre Sylva, ya riga mu gidan gaskiya.
Julius Bokoru, daya daga cikin hadiman tsohon ministan, ne ya sanar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ya fitar.
Wannan abin bakin ciki na zuwa ne yayin da ake tuhumar kanin marigayin kuma tsohon minista a Najeriya da hannu a yunkurin juyin mulki a kasar.
Asali: Legit.ng

