"Mun Gaji," Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Dakatar da Karatu a Jami'o'in Najeriya

"Mun Gaji," Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Dakatar da Karatu a Jami'o'in Najeriya

  • Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga sabon yajin aiki kan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan alawus din da ta yi alkawari
  • Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ya ce malaman jami'o'i gwamnatin tarayya sun gaji da jan kafar da ake yi
  • Shugaban ASUU ya ce ba zai yiwu gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniya sannan ta tilasta shugabannin jami’o’i su nemo kuɗin aiwatar da ita ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta yi barazanar sake shiga yajin aiki saboda rashin biyan wasu alawus-alawus da gwamnatin tarayya ta yi alkawari.

ASUU ta bayyana cewa muddin gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da take alkawuran da ta dauka, to ba ta da wani zabi illa ta umarci mambobinta su fara yajin aiki.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya kara tsanani, Gwamna AbdulRazaq ya zabi wanda zai gaje shi a 2027

ASUU.
Tambarin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) Hoto: @isumunna
Source: Twitter

Dalilin ASUU na komawa yajin aiki

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da The Cable a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2027.

Ya ce gwamnatin tarayya ta fara kokarin aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma kan alawus din Earned Academic Allowances (EAA) cikin “rudani da rashin tsari”.

Farfesa Piwuna ya bayyana cewa yanzu haka an kwashe watanni 18 ba tare da biyan alawus din EAA ba.

Yarjejeniyar da aka cimma da ASUU

Bayan kusan shekaru 16 ana fama da tsaiko wajen aiwatar da yarjejeniya tsakanin gwamnati da ASUU, gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar a ranar 14 ga Janairun 2026 domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki.

An ce an cimma yarjejeniyar ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin wakilan gwamnati da shugabannin ASUU, wanda aka kammala a watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Tana ƙasar waje: Lauyan Sadiya Farouk ya fadi abin da ya hana ta zuwa kotu

Sai dai tun daga watan Fabrairu ake samun jinkiri wajen biyan albashin malaman jami’o’i a jami’o’in gwamnatin tarayya.

Kungiyar ASUU ta gaji da jinkiri

Wannan lamari ya jawo korafe-korafe daga rassan ASUU a jihohi daban-daban, inda suka fara barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar gaba ɗaya ba.

Piwuna ya ce malaman jami’o’i sun gaji da abin da ya kira sakacin ma’aikatar ilimi wajen aiwatar da muhimman abubuwan da aka amince da su, musamman batun EAA.

Ya ce:

“Mambobinmu a rassan jihohi na jin raɗaɗin wannan matsala, saboda haka ana sa ran martaninsu. Ma’aikatar ilimi ta yi barci, muna son mu tashe ta."
Asuu da Tinubu.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Chris Piwuna da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956/X
Source: Facebook

Shugaban ASUU ya ce ba zai yiwu gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniya sannan ta tilasta shugabannin jami’o’i su nemo kuɗin aiwatar da ita ba, kamar yadda Punch ta kawo.

Ya ce an amince cewa za a haɗa EAA cikin albashin malamai domin kawo ƙarshen tarin bashin alawus-alawus, amma yanzu gwamnati ta sake komawa tsohuwar matsalar bashin EAA.

ASUU ta yi matsaya da gwamnatin tarayya

Kara karanta wannan

Trump ya nanata barazanar kawar da Iran daga doron kasa, ya fadi dalili

A baya, kun ji cewa kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 bayan dogo lokacin da aka shafe ana tattaunawa.

ASUU ta ce sabuwar yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga 1, Janairu, 2026, kuma an tsara duba ta a duk bayan shekaru uku domin tabbatar da an samu ci gaba.

Sabunta yarjejeniyar ta mayar da hankali sosai kan walwalar malaman jami’o’i, inda aka amince da karin albashi kashi 40 cikin 100 ga dukkan lakcarori.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262