Babbar Kotu Ta Hana Wani Kamfani Amfani da 'Naira' a Jikin Sunansa a Najeriya
- Babbar kotun tarayya ta umarci wani kamfani ya cire kalmar 'Naira' daga jikin sunan da yake amfani da shi domin kaucewa yaudarar jama'a
- Mai shari’arOmotosho ya bayyana cewa duk da cewa an yi wa kamfanin rijista tun shekarar 2004, sunan da ya zaɓa yana da ruɗani
- Kamfanin ne ya fara shigar da karar CBN kan amfani da kalmar 'eNaira' amma daflga bisani aka umarci ya sauya sunansa nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta haramta wa wani kamfani mai suna eNaira Payment Solutions Ltd ci gaba da amfani da kalmar 'Naira' a cikin sunansa.
Hakan na cikin hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun ya yanke ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2027.

Source: Twitter
Kotu ta amince da korafin bankin CBN
Premium Times ta ruwaito cewa kotun ta kuma amince da ƙorafin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shigar, tare da cin tarar kamfanin Naira miliyan 10.
Kotun ta umarci kamfanin da ya sauya sunansa nan take zuwa wani suna daban wanda ba ya ɗauke da kalmar “Naira”, watau sunan kuɗin ƙasar Najeriya.
Mai shari’ar Omotosho ya bayyana cewa duk da cewa an yi wa kamfanin rijista tun shekarar 2004, sunan da ya zaɓa yana da ruɗani kuma yana iya sa jama’a su ɗauka cewa yana da alaƙa da gwamnatin tarayya.
Dalilin hana amfani da kalmar 'Naira'
Ya ce dokar hukumar CAC ta ba hukumar damar hana ko umartar canza sunan kamfani idan sunan yana nuna wata alaƙa da gwamnati ko kuma zai iya yaudarar jama’a.
Tun farko, kamfanin ne ya shigar da ƙara a shekarar 2021 inda yake neman a hana CBN da CAC amfani da sunan “eNaira”, tare da neman diyyar sama da Naira biliyan 90.
Sai dai bankin CBN ya musanta ikirarin kamfanin, yana mai cewa “eNaira” wata kadara ce ta ƙasa kuma tana da alaƙa kai tsaye da kuɗin Najeriya wanda bankin ƙasa kaɗai ke da ikon sarrafawa.

Source: Twitter
Matsalar da kotu ta hango
Kotun ta kuma bayyana cewa idan aka bar kamfani mai zaman kansa ya mallaki sunan “Naira”, hakan zai iya haddasa rudani ga masu amfani da tsarin kuɗin intanet tare da barazana ga tattalin arzikin ƙasa.
Mai shari’ar ya ce:
“Duk wani kuɗi mai suna ‘eNaira’ zai sa mutane su ɗauka cewa kuɗi ne na hukuma da Babban Bankin Najeriya ke kula da shi.”
Kotun ta yanke hukuncin cewa kamfanin ba shi da ikon mallakar alamar “eNaira”, tare da umartar shi da ya daina bayyana kansa a matsayin mamallakin sunan, kamar yadda Vanguard ta kawo.
CBN ya kara kudin ATM a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo sauye-sauye, inda ya kara kudin mallakar katin ATM daga N1,000 zuwa N1,500.
Hakan ya nuna cewa CBN ya kara kudin da kashi 50 cikin 100 duk da yadda 'yan Najeriya ke kuka kan tsadar rayuwa da wahalar tattalin arziki.
Bugu da kari, bankin ya bayyana cewa ya soke tsarin karbar kudin kula da katin ATM na wata-wata da ake cire N50 daga asusun abokan hulda.
Asali: Legit.ng


