"Ku Zabe Ni"; Amaechi Ya Bayyana Shirinsa ga 'Yan Najeriya idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, na ci gaba da nuna da gaske yake yi wajen neman shugabancin Najeriya a 2027
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa kasar nan tana bukatar sabuwar hanya ta siyasa wadda za ta tsamo ta daga halin da take ciki
- Tsohon Ministan ya nuna cewa zai rage talauci da aikata laifuffuka idan aka ba shi damar zama shugaban kasar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana shirin da yake da shi ga Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Amaechi ya bayyana cewa Najeriya tana buƙatar sabuwar hanyar siyasa wadda ta ginu a kan rage talauci, samar da ayyukan yi, riƙon amana, da kuma bin doka da oda.

Source: Twitter
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a lokacin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise News.
Rotimi Amaechi ya ba 'yan Najeriya shawara
Amaechi ya ce dole ne ’yan Najeriya su fara auna shugabannin siyasa bisa la'akari da ayyukansu da kuma tarihin aikinsu maimakon ra'ayoyin ƙabila ko na shiyya.
A cewarsa, zaɓen 2027 kamata ya yi ya zama "kamar zaɓen raba-gardama" a kan dukkan ƴan siyasa masu neman muƙamai.
“Na kasance gwamna, minista, shugaban majalisar dokoki, kuma shugaban kungiyar gwamnoni. ’Yan Najeriya suna da ƴancin su auna ni bisa la'akari da ayyukana."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya ce gwamnatin Buhari ta gaza
Amaechi ya bayyana cewa ko da yake gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ta samu nasarori a wasu fannoni, ta kuma gaza wajen cika tsammanin jama'a da dama.
“A wasu fannoni mun samu nasara, kuma a wasu fannoni mun gaza wa ƙasar. Amma idan aka kwatanta da abin da ’yan kasa ke fuskanta a yau, abubuwa sun fi muni sosai a yanzu."
- Rotimi Amaechi
Yayin da yake waiwayar wa'adin mulkinsa na matsayin gwamnan jihar Rivers, Amaechi ya fito da batun zuba jari a fannin ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi, da kuma abubuwan more rayuwa na wutar lantarki.

Source: Facebook
Wane aiki Amaechi zai yi?
Bugu da ƙari, Amaechi ya yi alƙawarin goyon bayan duk wanda ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, muddin tsarin ya kasance bayyananne kuma abin gaskatawa.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su kare ƙuri'unsu a lokacin zaɓubbuka kuma su jure ka da a karkatar da sakamakon zaɓe.
“Ku zaɓe ni saboda zan rage talauci kuma zan rage aikata laifuka. Na taɓa yin hakan a jihar Rivers, kuma zan iya sake yin hakan ga Najeriya."
- Rotimi Amaechi
Mai neman zama shugaban kasa yana kukan yunwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya koka kan matsalar yunwa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Amaechi ya bayyana cewa yana fuskantar matsin rayuwa irin na sauran ‘yan Najeriya, yana mai cewa akwai kwanakin da yake komawa gida ba tare da abin da zai ci ba.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana nufin “yunwar mulki” ne, sai ya ce ya ka da baki ya bayyana cewa yunwar abinci yake nufi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

