FBI Ta Gano Yadda Matasa Suka Hadu aka Kitsa Mummunan Hari kan Masallaci a Amurka
- Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI ta fitar da bayani kan wasu matasa biyu sun kai hari a wani masallaci da ke San Diego
- Hukumar ta tabbatar da cewa matasan da ke da shekaru 17 da 18 a duniya sun kai harin da ya yi sanadin rasuwar akalla mutane uku a masallacin
- FBI ta cbayyana yadda matasan suka hadu, da kuma yadda suka rika musayar maganganu na nuna tsantsar tsana ga Musulmai da wasu mutane a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
California, USA - Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) ta bayyana cewa wasu matasa biyu masu shekaru 17 da 18 da suka kai hari wani masallaci a birnin San Diego na jihar California da ke Amurka.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an gano cewa matasan sun samu tsattsauran ra’ayi ne ta yanar gizo kafin su aikata harin da suka shirya a tsanake.

Source: Facebook
Rahoton kamfanin dillancin labarai na AP ya ce matasan sun kashe mutum uku a cibiyar addinin Musulunci ta Islamic Center of San Diego kafin daga bisani su kashe kansu a cikin wata mota da jami’ai suka gano kusa da wurin.
Maharan masallacin Amurka sun ki jinin Musulmi
Sky News ta ruwaito cewa babban jami’in FBI a San Diego, Mark Remily, ya ce matasan sun nuna kin jinin Muslmai, amma ba su takaita ƙiyayyarsu ga wata ƙungiya guda ba.
Ya ce:
“Ba su nuna bambanci kan wanda suke ƙi ba.”
Takardun rubuce-rubuce da jami’an tsaro suka gano sun nuna cewa matasan suna nuna ƙiyayya ga Yahudawa, Musulmai, baƙar fata, mata da kuma masu rajin auren jinsi.
Rahoton ya ce matasan sun yi amfani da kalamai da alamomin da ake dangantawa da masu ra’ayin fifikon fararen fata da kuma Nazis.
FBI ta gano kungiyar mahara masallaci
Haka kuma, sun kira kansu da suna “Sons of Tarrant,” suna nuni da wanda ya kai harin masallatai a Christchurch na ƙasar New Zealand a shekarar 2019 inda aka kashe mutane 51.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun far wa mutane bayan sun dawo daga sayayyar kayan Sallah a Katsina

Source: Facebook
Limamin masallacin San Diego, Imam Taha Hassane, ya bayyana cewa wani jami’in tsaro mai suna Amin Abdullah ya yi artabu da maharan domin hana su shiga ajujuwan makaranta da yara 140 ke ciki.
Ya ce Amin Abdullah ya yi amfani da na’urar sadarwa wajen sanar da jami’ai a kulle wurin kafin daga bisani ya rasa ransa.
A cewarsa:
“Ya sadaukar da rayuwarsa domin hana su shiga cikin ajujuwan.”
Jami’an bincike sun kuma gano bindigu, harsasai da baka mai harbi a gidajen da ake zargin maharan suna amfani da su.
FBI ta ce matasan sun fara haɗuwa ne ta yanar gizo kafin daga baya su gano cewa dukanninssu suna zaune ne a yankin San Diego.
Hukumar makarantu ta San Diego ta ce ɗaya daga cikin matasan yana karatu ta intanet tun shekarar 2021 kuma ana sa ran zai kammala makarantar sakandare a wata mai zuwa.
Kungiyoyin Musulman Amurka sun nuna damuwa kan yadda kalaman ƙiyayya ga Musulmai ke ƙaruwa a fadin ƙasar.
An kai wa Musulmi hari a Amurka
A baya, mun kawo labarin cewa mutane uku sun mutu bayan wani harin bindiga da aka kai masallacin cibiyar addinin Musulunci ta San Diego da ke California a kasar Amurka a ranar Talata 19 ga watan Mayu, 2026.
Jami’an tsaro sun ce ana binciken harin a matsayin 'harin kiyayya ga Musulmai', yayin da wadanda ake zargi - wasu su biyu suka hallaka kansu bayan kisan mutane uku gabanin zuwan jami'an tsaro.
Wani jami’in tsaron masallacin mai suna Amin Abdullah ya rasa ransa yayin da yake kokarin kare jama’a daga harsasan 'yan bindigar tare da gaggawar sanar da makarantar cewa a kulle ajujuwan dalibai
Asali: Legit.ng

